Yadda hatsarin jirgin ƙasa ya rutsa da motar BRT a Legas

0
432

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas ta ce mutum biyu daga cikin waɗanda haɗarin jirgin ƙasa da ya rutsa da motar safa ta BRT sun mutu.

Daraktan sashen hulɗa da jama’a da wayar da kan jama’a na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas, Adebayo Taofiq, ya shaida wa manema labarai cewa motar bas din na cike maƙil da ma’akatan gwamnatin jihar Legas inda ya ƙara da cewa direban bai haƙura ba lokacin da ya hangi tahowar jirgin.

Ya ce, “Ba za a iya lissafin adadin ma’aikatan da ke cikin motar ba cikin sauki; domin wasu na tsaye ne a cikin motar saboda motar bas ce mai cike da kaya da fasinja, ya ce ya kamata direban ya jira jirgin ya wuce amma sai ya yi garaje.

KU KUMA KARANTA: Jami’an tsaro sun ceto mutane 6 da aka yi garkuwa da su a jirgin ƙasa a Edo

Ya ce a lokacin da jirgin yayi haɗarin bai kai ƙarfe 8 na safiyar Alhamis ba, don haka garaje ko gaggawar me yake?

“Mutane biyu ne suka mutu kuma jirgin ya ja motar zuwa wani wuri yayin da wasu kuma suka yi saurin tsalle daga cikin bas yayin da wasu suka makale.

“Za mu iya cewa an ceto mutane 15 a yanzu. Ba za mu iya bayar da ainihin adadin ba amma mutane biyu sun mutu.

“Tun da farko Taofiq ya tabbatar da faruwar hatsarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce, “A safiyar ranar Alhamis ne wata motar ma’aikatan gwamnatin jihar Legas mai lamba 04A- 48LA, da jirgi ya murƙushe a unguwar PWD da ke yankin Ikeja a Legas.

“Hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama yayin da motar bas din ta cika makil da ma’aikatan gwamnati da ke kan hanyar ofishinsu da safiyar yau.”In ji sanarwar.

Wata da ta shaida lamarin, da ta zo neman magani a asibitin koyarwa na jami’ar Legas (LASUTH) amma ba ta so a ambaci sunanta ta bayyana lamarin a matsayin “abin tausayi.”

“Na isa LASUTH da ƙarfe 8 na safe don duba idona, an gaya min jirgin ya tawo Muhammad da babbar motar bas a PWD a lokacin da take ƙoƙarin tsallaka titin zuwa Ikeja, kuna buƙatar ganin taron jama’a a asibitin LASUTH da waɗanda suka ji rauni duk sun jike cikin jini.

An shigo da su da wannan motar ta asibiti, Ba zan iya tsayawa ina kallo ba saboda wurin ya kasance mai zubar da jini da raɗaɗi.

Har yanzu suna kawo ƙarin mutane, ”in ji ta.

Leave a Reply