Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a jihar Ogun, Olufemi Oguntoyinbo, a ranar Asabar, ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi watsi da bayanan ƙarya da ake yaɗawa cewa ya fice daga jam’iyyar siyasa a jihar.
Oguntoyinbo, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kan sa, ya ce har yanzu yana nan kan fafutukar ‘yantar da al’ummar jihar daga hannun injinan siyasa, waɗanda jarin kasuwancinsu, farfaganda ce ta siyasa.
Ya bayyana wannan jita-jita da cewa ba gaskiya ba ne, kuma zagon ƙasa ne da jam’iyyun adawa ke yi don ɓata sunan sa da ke ƙara haɓɓaka.
“Jam’iyyar NNPP ta kasance jam’iyya daya tilo da ke da muradin talakawa, matasa da kuma jam’iyyar da za ta ba matasa ilimi kyauta da kuma samar da guraben aikin yi ga kowa da kowa.
KU KUMA KARANTA: EFCC ta Kama Ɗan takarar Jam’iyyar NNPP a Kogi
“Jita-jitar cewa na fice daga takarar gwamna a jihar Ogun ba gaskiya ba ne, kuma baƙar magana ce kawai. Jam’iyyar NNPP har yanzu tana cikin tseren.
“Bayan da na zagaya dukkan ƙananan hukumomi 20 da ke jihar, matakin karɓuwar da na samu daga masu zaɓe ya sanya sauran jam’iyyun siyasa tada zaune tsaye, don haka, buƙatar ‘yan siyasa su zaɓi farfagandar siyasa, ƙarya, yaɗa bayanan ƙarya da yaudara.”
Oguntoyinbo ya ci gaba da cewa al’ummar jihar sun riga sun san halin da wasu ‘yan siyasa ke yi wanda ba za su iya kai su ko’ina ba a zaɓen gwamna.
Ɗan takarar gwamnan na NNPP ya ce, “Ina so in yi amfani da wannan hanyar domin in yaba wa waɗanda suka yi imani da iyawa da ƙarfina wajen ciyar da jihar gaba.
“Ina so in tabbatar wa mutanen jihar Ogun cewa ba ni cikin wata tattaunawa da wata jam’iyya ko ɗan takara, har yanzu ina cikin takara kuma nasara tamu ce,” in ji shi.
[…] KU KUMA KARANTA: Ban janye takarata ba, inji ɗan takarar gwamnan jami’yyar NNPP a Ogun […]