INEC ta ɗage tattara sakamakon zaɓe har zuwa ƙarfe 2 na rana

0
324

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ɗage tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a ɗakin taro na ƙasa da ke Abuja.

Kwamishinan hukumar INEC na ƙasa, Festus Okoye, da karfe 12 na rana ranar Talata, ya ce za a ci gaba da tattara sakamakon zaben da ƙarfe 2 na rana.

Okoye ya bayyana cewa duk da cewa akwai sakamako daga jihohi biyar, hukumar na sa ran akalla wasu jihohi 10 za su shiga cikin shirin na yau.

A ranar Lahadi ne aka fara tattara sakamakon zaɓe daga jihar,taron na ranar Litinin ya ƙare ‘yan mintuna kaɗan daga karfe 10 na dare.

Shugaban hukumar INEC na ƙasa, Mahmood Yakubu ya dage taron zuwa karfe 11 na safiyar ranar talata domin baiwa jami’an tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihohi damar gudanar da zaɓen shugaban kasa a sauran jihohin da suka rage.

Sai dai da karfe 12 na rana Okoye ya yi magana da manema labarai inda ya ce an mayar da aikin tattarawa zuwa karfe biyu na rana a yau.

Tuni dai aka fitar da sakamako na kusan jihohi 14 tare da manyan jam’iyyun da ke raba nasara.

Bola Tinubu na jam’iyyar APC, ya lashe jihohin Ekiti, Oyo, Kwara, Ogun, Ondo, da kuma Jigawa.

Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya lashe jihohin Osun, Gombe, Yobe, Adamawa da Katsina.

Peter Obi na jam’iyyar LP ya lashe Legas, Enugu da Nasarawa.

Leave a Reply