Connect with us

'Yansanda

Sauya ƙuɗi: Faɗa ya ɓarke a Legas

Published

on

Faɗa ya ɓarke a wasu yankuna a kan babbar hanyar Legas zuwa Ikorodu a jihar Legas, kan karancin kuɗin sabbin Naira da kuma wahalhalun da manufar ta jefa ‘yan Najeriya.

A safiyar ranar Juma’a ne dai wasu ɓata gari da ake wa laƙabi da ‘yar Ariya Boys a unguwar Mile 12 da Ketu da Ojota da ke kan titin Ikorodu suka kai farmaki kan matafiya tare da haifar da hargitsi.

Wani direban mota da baya son a buga sunansa saboda fargabar tsangwama, ya ce sai da ya koma ɗaya daga cikin tituna saboda hargitsin ya sauya hanya.

An cigaba da tada hargitsin ayankin tare da jin karar harbe-harbe.

A halin da ake ciki, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da tashin hankalin da ke faruwa a yankin Mile 12 na jihar Legas.

Ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Twitter a ranar Juma’a.

KU KUMA KARANTA:Yadda ƙarancin naira ya haddasa rikici a Ogun

Da yake mayar da martani ga wani sakon Twitter da ya nemi PPRO ya tabbatar da jita-jita, Hundeyin ya amsa, “Gaskiya ne. Mutanenmu suna can. An tura sassan ƙarfafawa. A zauna lafiya a can yayin da muke sa ido sosai da sarrafa lamarin. “

An kuma sami hargitsin a wasu sassan unguwar Agege sai dai wakilinmu ya shaida cewa zuwa yanzu ƙurar ta lafa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

'Yansanda

An ja hankalin ‘yan Najeriya kan shirin ƙungiyoyin asiri na ɗaukar sabbin mambobi

Published

on

An ja hankalin 'yan Najeriya kan shirin ƙungiyoyin asiri na ɗaukar sabbin mambobi

An ja hankalin ‘yan Najeriya kan shirin ƙungiyoyin asiri na ɗaukar sabbin mambobi

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ja hankalin ‘yan ƙasar game da shirin ƙungiyoyin asiri na ɗaukar sabbin mambobi a faɗin ƙasar musamman a jami’o’i da manyan makarantu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Jihar Ribas Grace Iringe-Koko ce ta yi wannan jan hankali a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar da maraice a birnin Fatakwal.

Ta bayyana cewa wata babbar ƙungiyar asiri ta Najeriya tana shirin gudanar da gagarumin biki ranar Lahadi a faɗin Najeriya, musamman a jami’o’i don tunawa da mutumin da ya kafa ta.

“Rundunar ‘yan sandan Jihar Ribas ta samu bayanai game da bikin da ƙungiyar Neo-Black Movement (NBM) za ta yi a faɗin ƙasar ranar 7 ga watan Yulin 2024. Ƙungiyar, wadda ake yi wa laƙabi da Aiye ko Black Axe, tana shirin gudanar da bikin ne domin tunawa da wanda ya kafa ta.

KU KUMA KARANTA: Shugaban hukumar leƙen asirin sojin Isra’ila ya yi murabus saboda harin Hamas na 7 ga Oktoba      

Bikin, wanda aka sanya wa suna Ranar AIYE ko 7/7 za a gudanar da shi ne a dukkan jihohin da ke faɗin ƙasa, musamman a manyan makarantu,” in ji sanarwar.

An gargaɗi masu ta da hankalin jama’a a Bikin Dodanni na Egungun a Jihar Oyo

Rundunar ‘yan sandan ta ce tana sane da munanan ayyukan ƙungiyar asirin na kisan mutane a manyan makarantu da faɗace-faɗace a tsakanin ƙungiyoyin asiri da tayar da zaune-tsaye da sauran manyan laifuka.

Ta ce yanzu haka ta baza ƙarin jami’an ‘yan sanda zuwa wasu wurare domin daƙile ayyukan ƙungiyoyin asiri, sannan ta yi ƙira ga iyaye su gargaɗi ‘ya’yansu su guji shiga ayyukan ƙungiyoyin asiri.

“Ana bai wa manyan makarantu shawarar ƙara matakan tsaro da kuma sanya idanu sosai domin tabbatar da tsaron dukkan ɗalibai.

Kazalika ana ƙira ga dukkan makarantu su lura da duk wani taro na ɗalibai da bai kwanta musu a rai ba,” a cewar sanarwar.

Continue Reading

'Yansanda

An tuɓe wa ’yan sanda 5 kaki kan karɓar cin hanci

Published

on

An tuɓe wa ’yan sanda 5 kaki kan karɓar cin hanci

An tuɓe wa ’yan sanda 5 kaki kan karɓar cin hanci

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tube wa wasu jami’an ta biyar kaki sakamakon zargin su da karɓar cin hancin kuɗi kimanin Naira miliyan uku.

Mataimakin Shugaban ’yan Sanda mai kula da Shiyya ta shida ta da ke Jihar Kuros Riba, Jonathan Towuru, ya sanar a Kalaba cewa ’yan sandan sun kwace kuɗin ne da bakin bindiga a hannun wani mai abin hawa.

A makon jiya ne aka zargi jami’an da ƙwayar kuɗin da bakin bindiga a hannun wani mutum da rundunar ta sakaya sunansa.

Yanzu haka waɗanda ake zargin an tuɓe masu kaki amma ana tsare da su ana bincike, da zarar an same su da laifi kotu za a turasu ta yanke masu hukuncin da ya dace.

KU KUMA KARANTA: ’Yan sanda za su tantance ’yan banga a Yobe

Mataimakin shugaban ’yan sandan ya ce waɗanda ake zargin su da karɓar cin hancin kuɗi Naira milyan uku daga wannun wani.

Ko a kwanan baya irin haka ta taba faruwa a kan babbar hanyar Kalaba zuwa Ikom inda aka kama wasu ’yan sanda kan karbar na goro.

Tafiya a kan hanyar na yawan zargin ’yan sanda da kula da shingen bincike a kan hanyar da yawan tatsar su kuɗi.

Continue Reading

'Yansanda

‘Yan sanda sun kama mutum 2 da ake zargin sace mahaifiyar Rarara

Published

on

Yan sanda sun kama mutum 2 da ake zargin sace mahaifiyar Rarara

‘Yan sanda sun kama mutum 2 da ake zargin sace mahaifiyar Rarara

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta sanar da cafke wasu mutum biyu bisa zargin hannu a garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara.

Mai magana da yawun rundunar a Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce “muna tsare da mutum biyu kan lamarin, muna ci gaba da bincike.”

Tun farko, Kwamishinan tsaro na Jihar Katsina, Nasiru Mu’azu ya ce an sace dattijuwar ce a daren Juma’a a ƙauyen Kahutu da ke Karamar Hukumar Ɗanja.

Mu’azu ya ce waɗanda suka sace matar sun yi hakan ta hanyar bi ta bayan gida, inda suka sace ta ba tare da jami’an da ke tsaron gidan sun sani ba.

Ya kuma bayyana cewa tuni aka tura jami’an tsaro waɗanda suka bazama cikin dazuka domin bin sawun ’yan bindigar.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar mawaƙi Rarara

Neptune Prime Hausa ta ruwaito shaidu a kauyen sun ce da misalin karfe daya na dare ne dandazon ’yan bindiga suka kutsa gidan dattijuwar suka yi awon gaba da ita.

“A kafa suka zo, ba su yi harbi ba a lokacin da suka ka yi awon gaba da ita cikin ’yan mintoci.

“Dattijuwar ba ta bijire musu ba a lokacin da suka memi ta biyo su.

“Duk da cewa ’yan bindigar sun samu wasu mutane a gidan, amma mahaifiyar Rarara kaɗai suka ɗauka.

“Babu wani yunƙuri da aka yi na tunkarar ’yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita saboda bindigogin da suke ɗauke da su,” in ji wani mazaunin ƙauyen na Kahutu.
Ya ce, “Watakila maharan sun bar baburansu ne daga nesa suka tako zuwa cikin ƙauyen a kafa.

“Muna rokon Allah Ya kuɓutar da ita cikin koshin lafiya domin tana taimaka mana sosai a wannan ƙauyen.

“Danta Rarara mai yawan taimakon al’umma ne, kuma ya kawo mana abubuwan ci gaba sosai a garinmu,” in ji shi.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like