Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa wasu jami’an gwamnatin tarayya a fadar Aso Rock Villa na ƙoƙarin tada zaune tsaye a kan nasarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, tare da ƙokarin dusashe nasararsa a babban zaɓen da za a yi a watan nan.
El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.
Ya ce, “Na yi imanin akwai wasu mutane a cikin Villa da ke son mu faɗi zaɓe saboda ba su samu ba; suna da ɗan takararsu, ɗan takararsu bai ci zaɓen fidda gwani ba,” in ji El-Rufai.
A cewar gwamnan Kaduna, waɗanda ke adawa da nasarar Tinubu su ne mutanen da Tinubu ya kayar da ’yan takararsu na shugaban ƙasa a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar a bara.
El-Rufai ya ce makiyan Tinubu da ake zargin sun boye a ƙarƙashin manufofin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari don daƙile nasarar da tsohon gwamnan jihar Legas ya samu a zaɓen watan nan.
Ya ce, “Suna kokarin ganin mun faɗi zaɓe ne, kuma suna fakewa da burin shugaban ƙasa na yin abin da yake ganin ya dace.
KU KUMA KARANTA:PDP ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa Shugaba Buhari a Kano, ta ɗora laifin kan Tinubu da Ganduje
“Zan ba da misali guda biyu: wannan tallafin man fetur da ake kashewa ƙasar tiriliyoyin Naira, wani abu ne da muka amince a cire.
“A gaskiya, na yi tattaunawa da shugaban ƙasa na nuna masa dalilin da ya sa ya tafi,domin ta yaya za ku iya samun babban kasafin kuɗi na naira biliyan 200 na titunan tarayya sannan ku kashe naira tiriliyan 2 wajen tallafin man fetur? Wannan tattaunawa ce da na yi da shugaban ƙasa a shekarar 2021 lokacin da abin tallafin ya fara tashi, ya gamsu, mun tafi.
“Kowa a cikin gwamnati ya yarda, kuma ya canza, misali na biyu da zan bayar shine sake fasalin kuɗin.
“Dole ne ku fahimci shugaban,jama’a suna zargin Gwamnan babban bankin ne da laifin sake fasalin kuɗin, amma a’a sai dai ku koma ku kalli ficewar Buhari a matsayin shugaban ƙasa na farko.
“Ya yi wannan; gwamnatin Buhari da Idiagbon sun canza mana kuɗin mu kuma sun yi su a asirce da nufin kamo waɗanda ke wawure kuɗaɗen haram, niyya ce mai kyau.
Shugaban kasa yana da hakkinsa, amma yin hakan a wannan lokaci a cikin lokacin da aka ba shi ba ya da wata, ma’ana ta siyasa ko tattalin arziki.”