Saboda masu tara kuɗin haram muka sauya takardun kuɗi, inji Buhari

1
476

Ba don Talaka muka sauya kuɗi ba, sai don mutnen da suka tara kuɗin haram, inji Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an inganta rabon sabbin kuɗaɗen Naira.

A wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban ƙasa ya fitar a ranar Asabar, shugaban ya ce an yanke shawarar sake fasalin naira ne domin magance tarnaki na haramtattun kuɗaɗe.

Yayin da yake amsa rahotannin kan dogayen layuka a bankunan, Buhari ya ce babban bankin Najeriya (CBN) yana aiki kan shirye-shiryen “hana hargitsi” kan rabon sabbin takardun kuɗi.

KU KUMA KARANTA:CBN zai hukunta duk bankunan da ke ɓoye sabbin kuɗi

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Asabar ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa ‘yan ƙasa basu da wata matsala a harkokin kasuwancin su kuma ba za a samu cikas ba ga dukkanin hanyoyin samar da kayayyaki da suka taso daga musayar kuɗin da zai kawo ƙarshe nan ba da dadewa ba,” in ji sanarwar.

“Da yake mayar da martani kan wasu dogayen layukan da aka yi na jiran mutane na tsawon sa’o’i kafin su iya ajiye tsofaffin takardun kuɗi su samu sababbi, lamarin da ya jawo fushin jama’a da sukar ‘yan adawa, Shugaba Buhari ya sake bayyana cewa an yi canjin kuɗin ne domin mutane da suka tara kuɗaɗen haram ba wai talaka ba. , da kuma cewa ya zama dole a hana jabu, cin hanci da rashawa, da tallafin ‘yan ta’adda.

“Wannan, in ji shi, zai daidaita da kuma ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar.

“Yayin da yake lura da cewa mafi yawan al’umma na fuskantar ƙunci domin sau da yawa sukan ajiye maƙuɗan kuɗaɗe a gida don kashe su, shugaba Buhari ya ba da tabbacin cewa gwamnati ba za ta bar su ga makomarsu ba.

“Ya sake nanata cewa akwai shirye-shirye da dama daga babban bankin kasa da kuma dukkan bankunan kasuwanci don hanzarta rarraba sabbin takardun kuɗi da kuma yin duk abin da ya dace don daƙile taɓarɓarewar kuɗi da hargitsi.”

1 COMMENT

Leave a Reply