Tsoffin Kuɗi: Bankunan First bank da GTB sun cigaba da aiki har ranar Asabar da Lahadi

1
343

Rasdan bankunan First Bank da Guarnty Trust Bank faɗin ƙasar nan sun fara aiki a ranakun asabar da lahadi domin karɓar tsofaffin takardun kuɗi na naira kafin wa’adin da babban bankin Najeriya ya ƙayyade a ranar 31 ga watan Janairu.

A wata sanarwa da mahukuntan bankunan suka fitar a ranar Juma’a, sun ce aikin da aka shirya gudanarwa a ƙarshen mako na karɓar tsofaffin takardun naira ne kawai.

“Wannan shine don sanar da jama’a cewa za a buɗe dukkan rassan mu a ranakun asabar da lahadi domin karɓar kuɗi.

KU KUMA KARANTA:Mun bada isasshen lokaci don haka babu ja da baya kan daina karɓar tsoffin kuɗi- CBN

“Dukkan tsofaffin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da 1000 za su daina amfani da su daga ranar 31 ga watan Janairu,” in ji First Bank a cikin sanarwar.

CBN ta dage cewa za a daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi na N200, N500 da N100 daga ranar 31 ga watan Janairu.

Gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele, ya ce wa’adin ya ci gaba da kasancewa a yadda ya ke, duk da kiraye-kirayen da masu ruwa da tsaki suka yi na cewa babban bankin ya ƙara wa’adin.

1 COMMENT

Leave a Reply