Gwamnatin jihar Kwara ta bada hutu yau ranar Laraba , a matsayin ranar da babu aiki ga ma’aikatan gwamnatin jihar don su sami damar karɓar katin zaɓe na dindindin, domin su taka rawar gani a zaɓukan dake tafe.
Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugabar ma’aikata ta jihar, Uwargida Susan Oluwole, a ranar Talata, ta shawarci waɗanda har yanzu ba su karɓi katin zaɓensu na dindindin a (PVC), da su yi amfani da damar hutun su yi hakan.
Oluwole ta ce, “Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak, ya amince da yau Laraba 25 ga watan Janairu, 2023, a matsayin ranar da babu aiki ga ma’aikatan jihar.
“Wannan shi ne ze bai wa ma’aikata isasshen lokaci domin su samu katin zaɓe daga INEC domin su samu damar taka rawa sosai a babban zaɓe mai zuwa.
KU KUMA KARANTA:An Kama barayin katin zaɓe 158 a Kano
“Ana gargaɗin duk waɗanda har yanzu ba su samu katin zaɓe ba da su gaggauta yin hakan kafin lokaci ya ƙure.”
Har ila yau, gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, a ranar Talata, ya yabawa ‘yan ƙasar bisa yawan fitowar da suka yi na karbar katinan su na PVC.
A karshen makon da ya gabata ne gwamnan ya ayyana ranar Talata a matsayin ranar da babu aiki don baiwa mazauna yankin damar karɓar katinan su na PVC, Oyebanji, wanda ya samu wakilcin mataimakiyarsa, Uwargida Monisade Afuye, ya bayyana haka a yayin wani atisayen sa ido domin tabbatar da bin umarnin gwamnatin jihar na masu rijistar na karbar katinan su na PVC.
Ya ci gaba da cewa, “Muna zagayawa ne domin manufar da aka ayyana wannan hutun ta cika, kuma ba mu da wani dalilin yin nadama da yawan masu rajista da muke gani a duk ofisoshin INEC da na ziyarta.
“Dukkanku kun san cewa rashin tausayin masu kaɗa kuri’a ya kasance haɗari ne a zaɓukan ƙasar nan kuma wani yunƙuri ne na wannan gwamnati ta magance wannan matsala da jihar ta ayyana a yau a matsayin ranar hutu domin jama’armu su karɓi katin zaɓe na PVC domin su shiga duk zabe. ”
Ƙugiyar Ohanaeze ya ba da shawara;
A halin da ake ciki, kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta ɗorawa ƙungiyoyin ƙwadago na gari a dukkan al’ummar Igbo da su fara aiwatar da manufa mai taken ‘no PVC, no rights’, wato babu PVC babu ‘yan ci.
Ƙungiyar koli ta al’adun kabilar Igbo ta bayar da wannan shawarar a ranar Talata yayin da ta yaba wa gwamnan jihar Ebonyi da kuma shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, David Umahi, kan matakin da ya ɗauka na ayyana hutun kwanaki biyu domin baiwa ma’aikatan jihar damar samun katinsu na PVC.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar Ohanaeze ta kasa, Dr Alex Ogbonnia, ta nuna cewa ya kamata a ba da fifikon cewa kada wani ɗan kabilar Igbo na gaske da ya bari muradin cikin gida, ko na sirri, ko son kai su tsallake muradun gamayya na Igbo a zaɓe mai zuwa.
A wani bangare ya ƙara da cewa, “Muna kira ga kungiyar gamayyar garuruwan Kudu maso Gabas ƙarkashin jagorancin Cif Emeka Dive da su yi amfani da karfinsu wajen aiwatar da manufar ‘ba PVC, babu ‘yancin al’umma.
“Don haka, Ohanaeze ta bambanta tsakanin yakin neman zaɓe mai karfi da gwagwarmayar kafofin sada zumunta a ɓangare guda da kuma kaɗa kuri’a yayin zaɓe a ɗaya ɓangaren.”