‘Yar Ganduje ta sha alwashin mayar da sadakinta N50,000 da mijinta ya bayar na aurenta

Asiya Ganduje, ‘yar gwamnan Jihar Kano, a ranar Alhamis, a gaban wata Kotun Shari’a, ta dage cewa za ta maido da kuɗin sadaki Naira 50,000 da mijinta, Inuwa Uba ya biya, don kawo ƙarshen aurensu na shekara 16.

Ɗiyar gwamnan da ta shigar da ƙarar, ta kasance a gaban kotu tana neman a raba aurenta, ta hanyar Musulunci (Khul’i) saboda ta yi ikirarin cewa ta gaji da zama da mijinta mai suna Inuwa.

Lauyan wanda ya shigar da ƙara, Ibrahim Aliyu Nassarawa, ya shaida wa kotun cewa wanda yake karewa ta dage sai ta mayar da kuɗin sadakin ta Naira 50,000 da aka karɓa daga hannun mijinta domin a raba auren.

“Kowace macen da ke rayuwa a cikin wani yanayi na rashin jin daɗin auranta, tana da haƙƙi a tsarin shari’ar Musulunci ta garzaya kotu ta nemi a raba aurenta da sharadin mayar da sadaki”.

KU KUMA KARANTA:‘Yar Ganduje ta shiga cikin badaƙalar saki

“Wanda nake karewa a shirye take ta mayar da kuɗin sadakin N50,000 da aka karba, domin a raba aure.”

Aliyu Nassarawa ya ce wanda yake karewa bata gamsu mijinta na sauke hakkinta ba kuma ba zai bi sharuɗɗan da aka gindaya masa ba.

“Sharuɗɗan su ne batun rikicin da ya kamata a shigar da shi a gaban wata kotu.”

Tun da farko, Lauyan wanda ake ƙara, Umar I. Umar, ya ce batun ya wuce biyan sadakin N50,000.

“Wanda nake karewa yana da sharuɗɗa biyu dangane da wasu kayansa, kafin a zo batun saki.

“Wanda ake ƙara yana da ‘ya’ya hudu tare da mai ƙarar, amma duk kokarin sulhun hakan ya ci tura.

“Ya kamata mai ƙara ta mayar da duk takardunsa, da takardun shaida na gida, da motoci, sannan ya sauke mata hakkinta a kamfaninsu na shinkafa.”

Alkalin kotun, Malam Halliru Abdullahi, bayan ya saurari bayanan ɓangarorin biyu, ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 2 ga watan Fabrairu mai zuwa domin yanke hukunci.

A ranar 12 ga watan Junairu ne kotun ta yi watsi da ƙarar farko da lauyan ya shigar ga wanda ake ƙara, inda yake kalubalantar hurumin kotun na sauraron ƙarar.


Comments

One response to “‘Yar Ganduje ta sha alwashin mayar da sadakinta N50,000 da mijinta ya bayar na aurenta”

  1. […] KU KUMA KARANTA:‘Yar Ganduje ta sha alwashin mayar da sadakinta N50,000 da mijinta ya bayar na aurenta […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *