Yadda wani mutum shaƙe budurwarsa saboda cin amana, ya kuma cinna wa kansu wuta

3
602

Wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Baby Face ya mutu a wata gobara da ake zaton ya tayar a gidansa da ke ƙaramar hukumar Oyigbo a jihar Ribas, inda aka tsinto gawar budurwarsa da har yanzu ba a tantance ko wacece ba

Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya gayyaci masoyiyarsa zuwa gidansa da ke Kom Kom, wani yanki mai dimbin jama’a a Oyigbo, a wajen garin Fatakwal a karshen mako, lokacin da lamarin ya faru.

Wata majiya ta ce daga baya mutumin ya yi wa budurwar tambayoyi kan wata alaƙa da ta yi da wani mutum, lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin masoyan.

Wani da ya shaida lamarin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce daga baya mutumin ya shaƙe budurwar tasa.

KU KUMA KARANTA:Mahaifiyar matar da mijinta ya kashe akan biredi ta buƙaci adalci

Majiyar ta ce, “Bayan ya kashe yarinyar, sai ya cinna wa gidansa wuta domin yayi baddabanin kisan da ya aikata, amma wutar ta kama shi, ya ƙone da shi da gawar yarinyar a cikin gidan.”

Ya ce lamarin ya haifar da firgici a unguwar, yayin da mazauna unguwar suka bar wurin saboda tsoron kada ‘yan sanda su kama su.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta ce gobara ce ta tashi.

“Yarinyar ta mutu kuma an kai mutumin asibiti inda yake jinya, amma daga baya ya mutu.

“Mu (’yan sanda) mun ƙaddamar da bincike kan lamarin domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.

“Za mu bayyana sakamakon binciken mu ga jama’a,” in ji ta.

3 COMMENTS

Leave a Reply