Yadda mace ta yanke azzakarin mijinta, ta kashe shi har lahira

3
313

Wata mata mai suna Florencia Amado Cattaneo ta yanke azzakrin mijinta tare da daɓa masa wuƙa lamarin da yayi sanadiyar mutuwarsa.

An tsinci gawar mijin matar Pedro Federico Zarate mawaƙi da ya shahara da waƙoƙin aure da bushebushe a yankin Altos de San Lorenzo na ƙasar Ajantina.

Matar mai shekaru 41 da haihuwa, ‘yan sanda sun kama ta da laifin kisan gilla da ake zargin ta da aikatawa, kuma an tura ta ga likitoci don auna lafiyar kwakwalwarta, a cewar kafar yaɗa labarai ta internet ta Mail Online.

KU KUMA KARANTA:Yadda wani mutum ya kashe matar sa saboda burodi

Baya ga yanke al’aurar mijinta, ta kuma bar wata wuƙa binne a cikin kwayar idonsa.

An samu mamacin da wuƙar da matarsa ta caka masa a ido bayan ta yanke masa al’aura.

An kama wanda ake zargin wacce masaniya ce na ilimin halayyar dan adam, a ranar 11 ga watan Janairun 2023 bayan ta gudu zuwa gidan mahaifiyarta a cikin motar haya hannunta yayi ceɓe-cabe da jini, kamar yadda ‘yar uwarta Patricia ta shaida wa kafafen yaɗa labarai.

Ƙanwar matar ta tsinci gawar mijin a kan gado a gidan da suke zaune tare da matarsa ​​da ɗansa ɗan shekara biyar.

An tarar da raunuka daban-daban a jikin gawar, ciki har da kirjinsa, an kuma yanke masa al’aurar kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

An kwantar da wacce ake zargin a sashin kula da masu taɓin hankali na wata cibiyar kula da lafiya da ke La Plata, inda za a yi mata gwaje-gwaje.

Wanda aka kashe ya kasance mai shirya waka, ya kuma yi aiki a cibiyar al’adun lardin Estacion a La Plata tun 2006. Dan asalin Cordoba, ya auri matar da ake zargi da kashe shi a shekarar 2017.

3 COMMENTS

Leave a Reply