Yadda yaro ɗan shekara 17 ya yiwa mata 10 ciki

2
541

Jami’an ‘yan sandan jihar Ribas, sun kama wani yaro ɗan shekara 17 mai suna Noble Uzuchi, tare da abokin karawarsa, Chigozie Ogbonna, mai shekaru 29, bisa laifin yi wa mata 10 ciki a wasu gidajen ƙyanƙyasar jarirai.

Baya ga Uzuchi, da Ogbonna, ‘yan sanda sun kuma kama wasu mata biyu, Favour Bright mai shekaru 30 da Peace Alikoi kai shekaru 40.

A cewar jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, wadda ta bayyana kamen, mutanen huɗun sun yi aiki ne a ƙananan hukumomin Obio/Akpor da Ikwerre na jihar.

Kakakin rundunar ta ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan da aka samu labarin ta’asar tasu, ta ce an kuma ceto mata masu juna su 10.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da kwamitin yaƙin sha, da fataucin miyagun ƙwayoyi

“A ranar Asabar, 7 ga watan Janairu, 2023, da misalin karfe 4:45 na yamma, yayin da jami’an hukumar leken asiri ta C4I suka kai samame wasu gidaje biyu a unguwar Igwuruta da Omagwa, inda ake ajiye waɗanda ake yi musu fataucin yara.

“Wadanda aka ceto sun kai mutum 10, yawancinsu masu juna biyu ne.”

A cikin wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan ta fitar, ta ce bincike ya nuna cewa a lokacin da aka haifi jaririn , mai masana’antar yin jariran na karɓe yaran ya kuma ya biya uwar jaririn kuɗi naira dubu 500, ta ƙara da cewa, tuni aka sayar da wasu jariran da aka haifa a gidajen.

Ta ce, “Dukkan waɗanda abin ya shafa sun furta cewa an yaudare su ne da sayar da yara ba bisa ka’ida ba saboda suna buƙatar kudi duba da matsalolin da suke fuskanta.

An gano mota kirar Honda Pilot Jeep fara mallakin mai gidajen ƙyaƙyasar jariran.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa an mika waɗanda ake zargi zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar (SCID) domin gudanar da bincike, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin zaƙulo waɗanda suka sayi yaran da aka riga aka sayar.

2 COMMENTS

Leave a Reply