Jami’an tsaro sun ceto mutane 6 da aka yi garkuwa da su a jirgin ƙasa a Edo

1
568

Gwamnatin Edo ta sanar da ceto shida daga cikin fasinjojin jirgin kasa 31 da aka sace ranar asabar, a ƙaramar hukumar Igueben da ke jihar.

Kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a na jihar, Chris Nehikhare ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Benin ranar Litinin.

A cewar Mista Nehikhare, mutanen da aka ceto sun haɗa da wani mutum mai shekaru 65, da uwa mai shayarwa da jaririnta, da wata yarinya ‘yar shekara 6 da ‘yan uwanta biyu masu shekaru biyu da biyar.

Ya kuma yabawa ƙungiyar agajin da ke cikin daji da ma’aikatan agaji da suka yi bakin kokarinsu wajen ganin an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su tare da sake haɗasu da iyalansu.

KU KUMA KARANTA:Harin Jirgin kasa: NAWOJ, Ta Yi Allah-Wadai Da Kakkausar Muryar Bisa Mummunar Ta’addancin

“Muna da tabbacin za a kuɓutar da sauran waɗanda lamarin ya rutsa da su nan ba da dadewa ba, saboda ƙwazon jami’an tsaro, kuma suna cikin ƙwarin guiwa kuma sun ruɓanya ƙoƙarin masu garkuwa da mutane” in ji shi.

Ya kuma nemi tallafafin masu ruwa da tsaki musamman kafafen yaɗa labarai.

Ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su ci gaba da kasancewa tare da gaskiyar lamarin tare da kaucewa rahotanni masu tada hankali, da za su iya ƙara haifar da raɗaɗi ga iyalai da abokan waɗanda abin ya shafa, waɗanda tuni suka shiga cikin ƙunci.

Ya kuma tabbatar wa mutanen Edo da sauran jama’a cewa waɗanda abin ya shafa za su dawo lafiya, yana mai cewa “ana ci gaba da aikin bincike.”

Kafanin dullancin labaran Najeriya wato NAN ta ruwaito cewa ɗaya daga cikin fasinjoji 32 da suka tsere daga hannun maharan, yana taimakawa jami’an tsaro wajen aikin ceto su.

1 COMMENT

Leave a Reply