Daraktan tuntuɓa da wayar da kai na ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima na yankin arewa maso yamma, Aminu Jaji, ya ce jam’iyyar APC ta gaji rashin tsaro da ƙasar nan ke fama da ita, don haka ba zai yu a iya ɗora alhakin akan ta ba.
Jaji, tsohon shugaban kwamitin leken asiri da tsaro na cikin gida a majalisar wakilai, kuma tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara a shekarar 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar APC, ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar.
Tsohon ɗan majalisar ya ci gaba da cewa gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an shawo kan matsalar tsaro.
KU KUMA KARANTA:APC ta ceto Najeriya daga wargajewa, Tunibu zai ɗora ya magance matsalar tsaro – Shinkafi
Jaji ya kuma ce yana da kwarin gwiwar cewa APC za ta yi nasara tare da rike kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 mai zuwa, ya kuma kara da cewa yana da yaƙinin cewa jihar Zamfara ma za ta kai APC ga gaci.
“Ina da ƙwarin gwiwar cewa APC za ta ci gaba da riƙe kujerar ta a matakin ƙasa da jihar Zamfara, kuma idan aka zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a 2023, zai sa Najeriya da ‘yan Nijeriya su yi alfahari.
“Na tabbata Sanata Bola Ahmad Tinubu zai ɗauki batun rashin tsaro a matsayin abin mafi fifiko kuma zai magance shi yadda ya kamata.
“Mun san cewa gwamnatin APC ce ta gaji matsalolin tsaro kuma jam’iyyar ta yi duk abin da za ta iya wajen magance matsalar,” inji shi.
Jaji ya kuma ce rijiyar man da aka gano a jihar Gombe da Bauchi an samu nasara a lokacin mulkin Buhari ne, wanda a cewarsa wata babbar nasara ce da gwamnatin APC ta samu.