Yadda matar Ronalado ta gwangwaje shi da dallelliyar mota a ranar Kirismeti

0
301

Tauraro, ɗan kwallon Portugal, Cristiano Ronaldo, ya samu kyautar Kirsimeti mai kayatarwa daga abokiyar zamansa, Georgina Rodriguez yayin da ta ba shi kyautar mota ƙirar Rolls Royce.

A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, tsohon ɗan wasan Manchester United ya nuna farin cikinsa yayin da matar tasa ta ɗauke shi tare da ‘ya’yansu ta nuna masa samfurin farar motar mai ratsin azurfar ƙirar Rolls Royce Phantom, wanda darajarta ta haura £250,000 kwatankwacin naira miliyan 134 da dubu 856 da naira 476.

Ɗan wasan mai shekaru 37 a duniya, a halin yanzu yana tattaunawa da ƙungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr ta ƙasar Saudiyya, kuma rahotanni sun bayyana cewa yana dab da ƙulla wata muhimmiyar yarjejeniya ta fam miliyan 175 da kungiyar a duk shekara.

KU KUMA KARANTA:Kulob din Saudi Arabiya ya yi tayin €300m ga Cristiano Ronaldo

Ronaldo dai ya sha fama da rashin lafiya shekara guda bayan da ya yi rashin jituwa tsakaninsa da Manchester United bayan wata fitacciyar hirar da ya yi da Piers Morgan

Ɗan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar ya kuma soke kwantiraginsa da United ta hanyar yarjejeniya da juna, bayan tattaunawar da ya yi da kocin kungiyar Erik ten Hag.

Ronaldo ya ce kulob din ya tsaya cak tun lokacin da Sir Alex Ferguson ya bar ƙungiyar a shekarar 2013, ya ƙara da cewa babu wani ci gaba ko kaɗan da kulob din ya samu.

Ya kuma ce ba ya mutunta Ten Hag, don haka manajan ba ya girmama shi. Haka kuma masu Man United, Glazers, sun sanar da cewa za su sayar da ƙungiyar kuma za su saurari tayi, bayan wasan kwaikwayo da Ronaldo.

Leave a Reply