Gwamnati zata sayar da rijiyoyin mai 7 da ke tsakiyar teku

0
196

Gwamnatin tarayya ta ba da tayin wasu rijiyoyin man fetir guda bakwai da ke cikin teku, inda ta yi ƙira ga masu zuba jari a duniya da su taho su saya.

Shugaban hukumar, kula da man fetur ta Najeriya, NUPRC, Engr. Gbenga Komolafe, ya bayyana hakan ne a ranar laraba yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Engr. Komolafe ya ce, wannan shi ne karon farko da ake gudanar tallan wani kadara mai zurfi a cikin teku bayan dokar masana’antar man fetur ta PIA a shekarar 2021, kuma tun daga watan Afrilun 2007 lokacin da aka ba da shinge 45 amma a ƙarƙashin dokar hana fita.

KU KUMA KARANTA:Sanata Saraki ya yi alkawarin bunkasa tattalin arziki, da soke tallafin man fetur

Hukumar ta CCE ta ci gaba da cewa, za a gudanar da taron tun kafin ranar 16 ga watan Junairu, 2023, kuma ana sa ran masu son zuba jari za su gabatar da takardar neman sayen rijiyoyin man a ranar 31 ga watan Janairu, 2023.

Leave a Reply