Ina marmarin komawa Daura – Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa yana fatan komawa Daura nan da watanni biyar masu zuwa, a ƙarshen wa’adinsa.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata ɗauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, Buhari ya shaida hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin ‘yan ƙungiyar Jam’iyyatu Ansaridden (Attijaniyya) a fadar gwamnati da ke Abuja.

Shugaba Buhari ya godewa ‘ya’yan ƙungiyar bisa gaggarumin addu’o’in da suke yi wa gwamnatinsa da kuma ƙasa, ya kuma yabawa ƙungiyar ta musulunci kan yadda ake ci gaba da yin hakuri akan al’amuran addini a kasar.

KU KUMA KARANTA:Amina Muhammad, Sakatare Janar ta majalisar Ɗinkin Duniya takai ziyara fadar shugaba Buhari

Sanarwar mai taken ‘Shugaba Buhari ya yabawa kungiyar Islama kan yadda suke ƙarfafa haɗin kan addini.

Garba Shehu ya ci gaba da cewa, “Shugaba Buhari wanda ya godewa ‘ya’yan ƙungiyar bisa gaggarumin addu’o’in da suke yi wa gwamnatinsa da kuma ƙasa baki ɗaya , ya ce yana fatan komawa garin Daura nan da watanni biyar masu zuwa a ƙarshen wa’adinsa.

Shugaban ya shaida wa ƙungiyar a ƙarƙashin jagorancin Khalifan Jam’iyyatu Ansarudden (Attijaniyya), Sheikh Muhammad Khalifa Niass, cewa ya yaba da rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a ƙasashen Afirka da dama.

A yayin ziyarar ban girma da kungiyar ta kai, Sheikh Tijjani Shehul Hadi Almauritany ya gabatar da addu’o’i ga shugaban ƙasa da kuma ‘yan Najeriya yayin da Sheikh Abdullahi Lamine ya gudanar da karatun kur’ani mai tsarki.

A nasa jawabin, Khalifan ƙungiyar, Sheikh Niass, ya ja hankali, kan tarihin Manzon Allah SAW, da irin darussan da musulmi za su iya koya daga tsarin rayuwarsa.

Da yake jaddada wajibcin tuba na gaske, kamar yadda koyarwar Alƙur’ani mai tsarki ta bayyana, Sheikh Niass ya yi alƙawarin cewa ƙungiyar Attijaniyya za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai, kamar yadda koyarwar littafi mai tsarki da musulunci suka tanada.

Khalifah Niass ya kuma ba da labarin irin kusancin da mahaifinsa, Sheikh Ibrahim Niass ya ke da ‘yan Nijeriya da al’ummarta, wanda ya kai shekaru saba’in yana mu’amalar arziki da su, inda ya ce iyalansa sun ƙuduri aniyar ci gaba da ƙulla alaƙa.


Comments

One response to “Ina marmarin komawa Daura – Shugaba Buhari”

  1. […] KU KUMA KARANTA:Ina marmarin komawa Daura – Shugaba Buhari […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *