Yadda Argentina ta lashe kofin duniya bayan ta doke Faransa

An shafe mintuna 120 ana nuna ƙwarewa inda Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya bayan da ta doke Faransa da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida a filin wasa na Lusail a gasar cin kofin duniya na FIFA da aka kammala a Qatar a yammacin lahadi.

Ƙwallaye biyu Lionel Messi da Angel Di Maria suka ci a minti na 22 da 36 ne suka sa Argentina ta ci gaba da jan ragamar Faransa kafin a tafi hutun rabin lokaci.

KU KUMA KARANTA:Morocco ta kafa tarihin zama ƙasar Larabawa da Afirka ta farko da ta tsallake zuwa wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya

Argentina dai ta ɗaure ne a minti na 80 da fara wasan inda tauraron Paris Saint-Germain (PSG) Kylian Mbappé ya farke kwallon da aka tashi 2-1. Faransa ta ci gaba da matsa lamba kan ‘yan wasan Argentina da watakila sun gaji wanda hakan ya sanya Mbappé ya zura kwallo a ragar wasan bayan daƙiƙa 60 kacal da kwallonsu ta farko.

An ci gaba da wasan a karin lokacin kuma Messi ne ya farke wa Argentina a minti na 108, inda aka tashi 3-2. Minti goma bayan haka, Mbappé ya amsa da ƙwallonsa ta uku inda aka tashi wasan.

A karshe dai bayan bugun daga kai sai mai tsaron gida takwas da hudu daga dukkan ƙungiyoyin biyu, Argentina ce ta fi yawan zura kwallaye hudu yayin da Faransa ta bata biyu inda aka tashi 4-2.


Comments

One response to “Yadda Argentina ta lashe kofin duniya bayan ta doke Faransa”

  1. […] KU KUMA KARANTA:Yadda Argentina ta lashe kofin duniya bayan ta doke Faransa […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *