A karo na biyu ‘yan bindiga sun kai hari kotun Imo, sun ƙona takardu

0
793

A ranar asabar ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a babbar kotun jihar Imo, da ke ƙaramar hukumar Orlu a jihar. An ce maharan sun kuma ƙona wasu muhimman takardu a harabar kotun da babban kotun da kuma kotun majistare.

Wannan na zuwa ne a karo na biyu da ‘yan bindigar suka kona kotun. A shekarar 2018 ne dai aka ƙona babbar kotun, kuma a ranar Asabar wasu mahara suka sake ƙona kotun.

A cewar ɗaya daga cikin shugabannin kotun, wanda ya yi magana a kan yanayin da ba a bayyana sunansa ba, ya ce, “Dukkan takardu, masu mahimmanci da ke cikin ginin sun ƙone.”

KU KUMA KARANTA:‘Yan IPOB sun bankawa ofishin INEC wuta, suka yi garkuwa da ma’aikata a Imo

Da yake jawabi shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Orlu, Barnabas Munonye, ​​ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Ya ce, sakataren gudanarwa na ƙungiyar ne ya shaida masa lamarin da safiyar asabar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abattam, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ƙara da cewa ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike kan lamarin.

Leave a Reply