Obasanjo tare da shugaban ƙungiyar yarbawa da Peter Obi sun ziyarci ƙugiyar Igbo ta Ohanaeze

0
505

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da shugaban ƙungiyar al’adun ƙabilar yarbawa ta Afenifere, Ayo Adebanjo da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, sun ziyarci hedikwatar ƙungiyar ƙabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo da ke jihar Enugu.

Sun kai ziyarar jaje ne ga ƙungiyar bisa rasuwar tsohon minista Mbazulike Amaechi a watan Nuwamba. Peter Obi, wanda ya tura hotuna ziyarar a kafafen sada zumunta, ya ce, “na haɗu da shugaba Obasanjo da Pa Ayo Adebanjo a hedikwatar Ohanaeze da ke Enugu, domin sanya hannu kan rajistar ta’aziyyar marigayi Cif Mbazulike Amaechi.
Tawagar ta samu tarba daga Cif Ogene Okeke” inji Peter Obi.

KU KUMA KARANTA:ABG Ya Yi Jimamin Tuna Rasuwar Janar Attahiru Yayin Da Ya Cika Shekara 1

A baya dai Marigayi, Amaechi ya jagoranci tawagar fitattun shugabannin al’ummar Igbo zuwa fadar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari domin neman a sako shugaban masu fafutukar kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu.

Leave a Reply