‘Yan sandan Gombe sun kama wasu matasa 4 bisa zargin yin garkuwa

2
284

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, ta ce ta kama wasu matasa biyu, bisa laifin haɗa baki da kuma yin garkuwa da matafiya biyu a hanyar Gombe zuwa Dukku.

Kwamishinan ‘yan sandan, Mista Oqua Etim, ne ya bayyana hakan, a lokacin da yake gabatar da waɗanda ake zargin tare, da wasu mutane shida a gaban manema labarai a karshen mako a Gombe.

Ya ce waɗanda ake zargin – Mamman Umar, ɗan shekara 20, ɗan tsohon yankin Liji a ƙaramar hukumar Yamaltu/Deba, da Abubakar Umar, mai shekaru 18, daga ƙauyen Bojude a karamar hukumar Kwami ta jihar,waɗanda hukumar leken asiri ta jihar (SIB) ta kama su.

KU KUMA KARANTA:Yadda ɗan shekara 12 yayi garkuwa da ‘yar shekara 3 a Bauchi

CP Etim ya ce a ranar 11 ga Nuwamba, 2022 ‘yan sanda sun samu ƙorafin cewa an yi garkuwa da mutane biyu; da Labaran Sabo mai shekaru 50 a ƙaramar hukumar Lafiya Lamurde ta jihar Adamawa, da Bala Yunana mai shekaru 33 a ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno a ranar 6 ga watan Nuwamba da misalin karfe 11 na dare yayin da suke kan hanyar wucewa a kauyen Bojude da ke kan hanyar Gombe zuwa Dukku, lamarin da ya sanya jami’an hukumar yin huɓɓasa inda suka kame matasan da ake zargi.

2 COMMENTS

Leave a Reply