Wani matashi da ya kashe budurwarsa don ya saci motarta ya shiga hannu

2
301

‘Yan sanda sun kama wani matashi mai suna Chidubem Osuagwu, mai shekaru 22, da ake zargi da laifin kisa da kuma sace motar buduwarsa mai shekaru 32 mai suna Amarachi Chukwu lamarin da ya abku a jihar Enugu.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe ne ya bayyana hakan, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ndukwe ya ce jami’an ‘yan sanda da ke aiki a sashin binciken kisan kai, na sashen binciken manyan laifuka na jihar Enugu, tare da aiki da jami’an ‘yan sanda a rundunar Imo, a ranar 8 ga watan Nuwamba, sun kama Osuagwu a unguwar Nekede na Owerri a jihar Imo.

KU KUMA KARANTA:Yadda ɗalibi ya kashe abokinsa bayan ya daɓa masa wuƙa a Bauchi

A cewarsa, yana yunƙurin sayar da wata mota kirar Toyota Corolla da ya sace daga hannun budurwarsa Chukwu, bayan ya kashe ta a ranar 1 ga watan Nuwamba a gidanta dake Meniru, Awkunanaw a cikin birnin Enugu.

“Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin da ‘yan tawagarsa gaba ɗaya, sun haɗa baki ne suka je gidan wanda aka kashen, suka yi yunkurin kwace mata mukullin motar ƙirar Toyota Corolla, wanda ta bijirewa hakan.

“Da ta ƙi yarda, sai suka ɗaure hannaye da ƙafafunta da bakinta da tsumma suka kulle ta cikin gidan sannan suka fice da motar.

“ An gano gawar ta a gidan da aka ce a ranar 4 ga watan Nuwamba, bayan da jami’an ‘yan sanda da ke aiki a sashin ‘yan sanda na Ikirike na rundunar, suka buɗe kofar da karfi, bayan samun rahoton cewa wani wari na fita daga cikin gidan.

“Jami’an ‘yan sanda sun ɗauki gawar zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar ta, tare da ajiye gawar a dakin ajiyar gawa, domin gudanar da bincike,” inji shi.

Kakakin ‘yan sandan ya ce an gurfanar da wanda ake zargin, a gaban kotu bayan kammala bincike, kuma an tsare shi a gidan yari na Enugu domin ci gaba da sauraron ƙarar.

2 COMMENTS

Leave a Reply