Tarihin Hadiza Aliyu Gabon

Hadiza Aliyu, wacce kuma aka fi sani da Hadiza Gabon,an haife ta a ranar 1 ga watan Yunin 1989 a Libreville, Gabon.

Ita ce ‘yar babban jigo, Malam Aliyu. Hadiza Aliyu ‘yar asalin ƙasar Gabon ce a bangaren mahaifinta, kuma asalin Fulani daga jihar Adamawa a Najeriya a bangaren mahaifiyarta.

Hadiza Aliyu ta yi makarantar firamare da sakandire a kasarta ta haihuwa, inda ta yi jarrabawar A-Level da nufin zama lauya, daga baya ta zabi Law a matsayin kwas din da ta fi so. Ta fara karatun a jami’a, amma karatun ya tsaya, saboda wasu dalilai da suka fi karfin ta, wanda hakan ya ba ta damar yin karatun difloma a cikin harshen Faransanci, daga baya kuma ta yi aiki a matsayin malamar Faransanci a wata makaranta mai zaman kanta.

KU KUMA KARANTA:Jarumar Kannywood Dawayya ta buɗe katafaren kantin sayar da kayayyaki a Kano

Ƙwararriyar yar wasan kwaikwayo ce kuma mai shirya fina-finai a Najeriya, wacce ke yin fina-finan Hausa da Turanci. Hadiza tana aiki a matsayin jakadiyar MTN Nigeria da kamfanin Indomie noodles. An zaɓi Hadiza mafi kyawun ‘yar wasa a shekarar 2013 (Best of Nollywood Awards).

Hadiza Aliyu ta shiga Kannywood ne bayan ta dawo Najeriya daga ƙasar Gabon, inda ta koma Kaduna da zama daga Adamawa, bayan ta yanke shawarar shiga masana’antar shirya fina-finan Kannywood tare da ɗan uwanta.

Hadiza Aliyu ta hadu da Ali Nuhu kwanaki kaɗan bayan ta isa Kaduna, inda ta nemi ya taimaka mata ta zama jaruma.

Hadiza Gabon ta fara fitowa a fim ɗin Artabu a shekarar 2009, kuma ta yi fice a matsayin ta na ɗaya daga cikin jaruman mata a masana’antar fina-finan Hausa.

Hadiza Aliyu, kamar Ali Nuhu, Sani Musa Danja, Yakubu Muhammed, Maryam Booth, da Rahama Sadau, ta shiga harkar Nollywood a shekarar 2017.Ta fito a fim ɗinta na farko na Nollywood, Legas Real Fake Life., tare da Mike Ezuruonye, Mark Angel, da Emmanuella.

Ta kuma ci lambar yabo ta Kannywood/MTN a karo na biyu a shekarar 2014, kuma yanzu haka tana aiki a matsayin wacce ta kafa gidauniyar HAG.

A watan Disamba 2018, NASCON Allied Plc, wani reshen rukunin Dangote ne ya bayyana Hadiza Aliyu Gabon a matsayin jakadiyar alamar Ɗangote Classic Seasoning a lokacin kaddamar da kayan kamfanin a Kano.


Comments

One response to “Tarihin Hadiza Aliyu Gabon”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *