‘Yan IPOB sun bankawa ofishin INEC wuta, suka yi garkuwa da ma’aikata a Imo

1
378

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar Biafra ta IPOB ne ko kuma ESN sun kona ofishin Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ke ƙaramar hukumar Orlu ta Jihar Imo, inda suka yi garkuwa da wasu ma’aikatan gine-gine. wadanda aka ceto daga baya.

Festus Okoye, kwamishinan hukumar ta INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a.

Kwamishiniyar zabe ta jihar Imo, Farfesa Sylvia Uchenna Agu, ta ce an kai wa ofishinmu da ke karamar hukumar Orlu hari, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 1 ga Disamba 2022.

“Ɓangaren sa, wanda ake kan gyare-gyarensa bayan harin da aka kai a baya, maharan sun lalata shi kuma suka ƙone wani bangare na ginin, sannan suka sace uku daga cikin ma’aikata bakwai da ke aikin gyaran, kafin daga baya suka sake,” inji Okoye.

KU KUMA KARANTA:Zaɓen 2023: An tsaurara matakan tsaro a ofisoshin INEC

Ya ce ɓarnar da ta fi haka,ba dan jami’an ‘yan sandan da suka yi gaggawar tura mutanensu zuwa wurin.

Wannan dai shi ne karo na huɗu da aka kai wa ofishin INEC hari cikin makonni uku da suka gabata.

A kwanakin baya ne aka ƙona ofisoshin INEC a Osun, Ogun, da Ebonyi, tare da lalata dubban katunan zabe na dindindin (PVCs), akwatunan zabe da sauran kayayyakin zabe.

“Wannan hari ya shafi wuri dayawa inda hukumar ta sake bayyana damuwarta kan yawaitar hare-haren da akan cibiyoyinta da kuma illar hakan akan shirye-shiryen zaben 2023” Okoye ya kara da cewa.

1 COMMENT

Leave a Reply