Tarihin Ali Jita da waƙoƙinsa

3
534

An haifi Ali Isa Jita ran 15 Yuli 1983, wanda aka fi sani da Ali Jita. Mawaƙin Hausa ne na Najeriya, kuma marubuci.

Ali Jita ɗan gidan Alhaji Sallau Jibrin Kibiya wanda mahauci ne, da mahaifiyarsa Hajiya Ummul-Khairi a unguwar Gyadi Gyadi da ke karamar hukumar Kumbotso jihar Kano a Najeriya.

Ya tashi ne a unguwar Shagari da ke unguwar Gyadi Gyadi. Yana yaro karami mahaifinsa ya kwashe iyalinsa daga Kano zuwa Legas, sannan ya koma Abuja saboda sana’arsa.

Ali Jita ya fara karatun Nursery/Elementary a Shagari Quarters. Sannan ya yi karatun firamare da karamar sakandare a Bonikam Barrack, Victoria Island, jihar Legas.

Ya kammala babbar sakandire a Abuja. Ya ci gaba da karatunsa a Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta Kano, inda ya samu takardar shaidar kammala difloma ta kasa kan harkokin gwamnati. Ya kuma karanci ilimin na’ura mai kwakwalwa a Intersystem ICT School inda ya samu shaidar difloma.

KU KUMA KARANTA:Jarumar Kannywood Dawayya ta buɗe katafaren kantin sayar da kayayyaki a Kano

Galibin waƙoƙin Ali jita ana amfani da su a masana’antar fim ta Kannywood, amma an sayar da wasu Album dinsa ga wasu masana’antun fina-finan Hausa.

Abokan aikinsa sun hada da Nazifi Asnanic, Fati Niger, Naziru M Ahmad, da dai sauransu, ya kuma haɗa kai da Umar M Shareef tare da shirya waka mai suna Mama, waƙarsa ta baya-bayan nan ita ce wakar ‘Kano’ a shekarar 2018. Waƙar Ali Jita mai suna Soyayya ce ta biyu mafi dadi wakokin Hausa na shekarar 2018 na BBC Hausa.

Ali Jita yana amfani da salon waka ta Ingausa, hade da Hausa da Turanci. Yana amfani da salon wajen rubuta waƙar da rera waƙa.
A shekarar 2019 ya fitar da faifan bidiyo na Arewa angel tare da wata jarumar Kannywood Rahama Sadau, ya kuma sake fitar da wani hoton bidiyon waƙar mai suna Soyayya da jaruma Hadiza Gabon,ya kuma shirya bikin sallah.

Ali Jita ya samu kyaututtuka da dama a harkar waka, lambobin yabo sun haura 15.

3 COMMENTS

Leave a Reply