Ba mu da kuɗin motar zuwa aiki – Shugaban ASUU

Shugaban ƙungiyar malaman Jami’o’i ta Najeriya, Farfesa Emmanuel Osodoke, ya ce mambobin ƙungiyar za su fuskanci wahala wajen komawa jami’o’insu a ranar Litinin saboda basu da kuɗin mota.

Shugaban na ASUU ya bayyana haka ne a jiya Lahadi, yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels dangane da janye yajin aikin na ASUU a cikin wani shiri mai suna Sunday Politics.

Farfesa Osodoke ya ce a lokutan baya malaman Jami’a na zama a gidajen da aka tanada musu kusa da makaranta, amma a yanzu ba haka lamarin yake ba domin suna zaune ne nesa da Jami’oin da suke koyarwa saboda yawancinsu basa samar musu wuraren zama.

“A can baya, malami zai iya taka wa da kafa yaje makaranta saboda suna zaune a cikin gidaje da aka tanada musu, amma a yanzu lamarin ya sauya, inda suke tafiyan kilomitoci 20 zuwa 30 kafin isa makaranta. Ta ya ya za su iya biyan kuɗin mota zuwa aiki,” in ji Osodoke.

Ya ce za su fuskanci wahalhalu wajen biyan kuɗin motar komawa aiki domin koyar da ɗalibai saboda ba a biya su ba har na tsawon wata takwas.


Comments

One response to “Ba mu da kuɗin motar zuwa aiki – Shugaban ASUU”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *