Gwamnatin Tarayya ta nemi afuwar ɗalibai da iyaye kan yajin aikin ASUU

0
472

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta nemi afuwar ɗalibai da iyayensu game da yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’a ta ASUU ta yi na wata takwas.

Cikin wata sanarwa, Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya tabbatar wa ɗaliban cewa “ba za ku sake fuskantar irin wannan matsanancin yanayin ba a nan gaba”.

Ƙungiyar ta Academic Staff Union of Universities (ASUU) ta tsunduma yajin aiki ne tun ranar 14 ga watan Fabarairun 2022 saboda neman a inganta rayuwar malaman. Ta janye yajin ne a ranar Alhamis sakamakon wani hukuncin kotu da ya umarce su su koma.

“Tun da ASUU ta yarda ta bi umarnin kotu na janye yajin aikin, muna neman afuwar ɗalibai da iyaye, wanda shi ma minista ɗaya ne daga cikinsu, kan wannan lamari da bai kamata ba tun farko,” a cewar sanarwar da Olajide Oshundun ya fitar a madadin Mista Ngige.

Leave a Reply