An kori ‘yan Najeriya 16 daga Ghana bisa laifin zamba ta yanar gizo

0
269

Aƙalla matasa ‘yan Najeriya goma sha shida (16) ne aka kora daga ƙasar Ghana bisa laifin da suka yi na aikata laifuka ta yanar gizo. Dr Chukwu Emeka, Konturola na Seme Command na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Juma’a, 14 ga watan Oktoba ya ce hukumar kuɗi da leƙen asiri a Ghana ta tuhumi mutanen da aka kora.

Dokta Emeka ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa an shawo kan wasu daga cikin yaran maza da mata a cikin aikata miyagun laifukan ne saboda cutar yin kuɗi yanzu yanzu nan da take samun wasu matasan Najeriya.

Emeka ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su riyka tafiya tare da ingantattun takardu, sannan kuma su riƙa gudanar da harkokinsu kamar yadda dokar ƙasar da suka je.

Yace; “Hukumar kula da harkokin kuɗi da leƙen asiri ta Ghana ta zarge su da aikata laifuka ta yanar gizo amma daga binciken farko da muka yi, mun gano cewa wasu daga cikinsu an ruguza su cikin wadannan ayyukan ta’addanci saboda matsalar rashin arziki da matasanmu ke fuskanta.

“Wasu daga cikin su abin ya shafa ne saboda an yaudare su cewa za su iya samun kudi idan sun bar Najeriya. Abin takaici, ba su sami ainihin abin da suka yi ciniki a Ghana ba. “Binciken da aka yi ya kuma nuna cewa sun bar ƙasar ta hanyoyin da ba bisa ka’ida ba ko kuma ta cikin teku zuwa wasu ƙasashen yammacin Afirka.”

Leave a Reply