Jami’ar Bayero ta Kano ta zama jami’a mafi inganci a arewacin Najeriya

0
394

Jami’ar Bayero, Kano (BUK), ta zama ta farko a Arewa, a jerin sunayen jami’o’in duniya na Times Higher Education 2023.

Kan gaba a jerin jihohin arewa, BUK ita ce ta huɗu a Najeriya, inda jami’ar Ibadan ta zama ta ɗaya a ƙasar. Jami’ar Legas ita ce ta biyu, yayin da Jami’ar Covenant ita ce ta uku a matsayi a Najeriya.

BUK, kasancewar ita ce Jami’a ta farko a Kano, an kafa ta ne a shekarar 1975. A halin yanzu tana da ɗalibai sama da dubu hamsin.

Jami’ar Oxford ta fito a matsayin mafi kyawun jami’a a duniya, sannan Jami’ar Havard, Jami’ar Cambridge Standford ta biyo baya.

Daliban BUK, tsofaffin daliban jami’ar, da wasu malaman jami’ar sun je dandalinsu na sada zumunta domin nuna murna da nasarar da aka samu.

Leave a Reply