JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
NASARAR da jagoran Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben fidda gwani da aka gudanar ya nunar da cewa gwamnan Jihar kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje shugaba ne mai kaunar ci gaban dimokuradiyya da zaman lafiya.
Wannan tsokaci ya fito ne daga wasu yan siyasa da suka zanta da wakilin mu, inda suka nunar da cewa ko shakka babu, gwamna Ganduje da takwarorin sa na arewacin kasar nan sun cancanci yabo da fatan alheri duba da yadda suka jajirce wajen ganin dimokuradiyya ta yi aiki a kasar nan.
Alhaji Usaman Dan gwari, wani fitaccen dan kasuwa, manomi kuma mai yin sharhi kan al’amuran yau da kullum yace kasarnan tana samun ci gaba ta fuskar dimokuradiyya, kuma ko shakka babu gwamna Ganduje da sauran gwamnon yan uwansa sun taka muhimmiyar rawar gani wajen ganin dimokuradiyya ta ci gaba da aiki a Najeriya.
Dan gwari ya yi amfani da wannna dama inda ya taya gwamna Ganduje murna bisa irin muhimmiyar rawar da ya taka wajen tabbatar da cewa an mutunta tsarin mika mulki ga kudancin kasar nan bisa tsari da sanin ya Kamata, tare da yin kira ga yan Najeriya da su ci gaba da kare martabar dimokuradiyya a wannan kasa.
Shima a nasa tsokacin, matashin dan siyasa, kuma jigo a jam’iyyar APC daga yankin karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Sa’adu Muktar Hayin Hago, ya jaddada cewa yanzu jam’iyyar APC a dunkule take, sannan akwai kyakykyawan zato cewa zata yi nasarar lashe zaben 2023, tare da taya sanatan kano ta Arewa Barau Jibrin da gwamna Ganduje murnar wannan gagarumar nasara.