Mu Ke Da Mulki Amma Mu Muke Shan Wahala Saboda Rashin Gaskiya – Sanata Bala Muhammad

0
711

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

DAN takarar Kujerar Shugabancin kasar Najeriya kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamaci al’ummar kasar nan musamman mutanen Arewa su fita daga cikin mawuyacin kangin halin ha’ula’i da suke ciki ta hanyar zabar wannan zai magance musu matsalarsu.

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bayyana hakan ne a yayin da kai ziyara Jihar Kaduna domin ganawa da wakilan Jam’iyyar PDP da neman amincewarsu na tsayar da shi a matsayin dan takarar Kujerar shugaban kasa na Jam’iyyar ta PDP.

Ya kara da cewa Jama’a na cikin wani yanayin da shugabancin Kasar ke da bukatar wani gogaggen gwarzon da yake tare da Jama’a kuma yasan makaman aiki kamar shi wanda zai iya taimakawa wajen ganin ya kwatowa al’umma yanci da hakkinsu ta hanyar basu walwala da jindadin mulkin Demokoradiyya.

Ya ce “ni tsohon mai’aikacin Jarida ne kuma tsohon mai’aikacin Gwamnati wanda ya yi aiki tun daga mataki na 8 har izuwa mataki na 17 matsayin Darekta kenan, sannan na yi zama Sanata da ministan babban Birnin Tarayya kana na yi zama Gwamna, don haka nake da kwarewa da gogewa.”

“Ba zamu zabi mutanen da zamu tura musu mota ta tashi su barmu da hayaki ba, domin mu muke da mulki amma mu muke shan wahala saboda rashin gaskiya don haka ba zamu Zuba Ido muna shan wahala ba, kuma na yi muku alkawari, muddun kuka zabe ni a matsayin Shugaban kasa, to za muyi aiki tare wajen gina al’umma da kasar wacce za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

“Mu a Arewa, shekara biyu kawai muka yi mulki wanda mai gidan bayan ya rasu muka mika mulkin ga mataimakinsa don ya gaje shi, kuma ita mulkin d ake yanzu ta APC tasu ba ta Jam’iyyarmu ba, don haka muna da sauran lokacin da za mu yi mulki wanda saboda haka ne yasa Uwar Jam’iyyar ta bude damar kowa zai iya tsayawa takara ba maganar Shiyya ko karba-karba na shiyya-shiyya.”

Acewar Kauran Bauchi, akalla su goma sha biyar ne ke neman Shugabancin Kasar a Jam’iyyar, kuma kowanne su kwararre ne, to amma ko daga cikin kwararrun akwai babban kwararre kuma shi ne wannan kwararren da al’ummar kasar ke bukata domin share musu hawayensu.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmad Makarfi, ya jinjinawa Dan takarar bisa ziyarar tare da bayyana cewa mutum ne Jajirtacce kuma mai cika alkawari da gogewa.

Acewarsa, mutum ne wanda bashi da tsoro kuma mai fadin gaskiya wanda Muddun ya ce zai yi abu, babu makawa zai aikata, kuma daga cikin mutanen da suke siyasa, ya kasance jarumi kuma Gwarzo.

A karshe, Sanata Makarfi ya shawarci Ya’yan Jam’iyyar ta PDP dasu ba da goyon bayansu wajen ganin ya cimma nasara na wannan kudirin nasa na neman shugaban kasa.

Leave a Reply