Isiguzo Ya Buƙaci Yan Jaridu Su Hada Kansu Yayin Ƙaddamar Da Ayyukan NUJ Kaduna

0
688

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

SHUGABAN kungiyar ‘yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), Kwamared Chris Isiguzo ya shawarci yan Jaridu da su rungumi hadin kai don cimma burin da aka sanya a gaba a cibiyar kungiyar ta Kaduna.

Isiguzo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga mambobin kungiyar (NUJ) reshen Jihar Kaduna yayin ziyarar Ƙaddamar da ayyukan da sabbin Shugabannin Kungiyar suka aiwatar a cikin watanni biyar da fara mulkinsu.

Kwamared Chris Isiguzo wanda ya tuno da munanan abubuwan da suka faru a lokacin tunkarar zaben Kungiyar da aka yi a watan Disambar da ya gabata, ya ci gaba da cewa babu wani ci gaba mai ma’ana da za a iya samu a cikin yanayi na tada zaune tsaye.

Shugaban ya bukaci shugaban Kungiyar da ta yi kokarin sasantawa ta rungumi sauran mambobin kungiyar da suka samu rashin jituwa lokacin zaben ta domin cibiyar na kowa da kowa ne don zama tsintsiya madauri daya.

Ya ce “ina rokon sauran Ya’yan wannan Kungiya da suke tunanin anyi musu badaidai ba, da su yi hakuri da dawo domin a ci gaba da zama daya, saboda babu ta yadda za ayi mutum ya guji gidansu, don haka nake roko ga kowa duka yan Jaridun da suzo a hada kai domin a gudu tare a tsira tare.”

“Ina godiya matuka ga Dattawanmu da suka ba da goyon bayansu wajen ganin cewa an aiwatar da al’amura yadda ya kamata kuma suka tabbatar da cewa gidan ba ta watse ba, don haka ina kira ga sauran Dattawan dake sauran cibiyar da su yi koyi da irin wannan natijan irin naku akoyaushe.”

Kwamared Isiguzo, ya bayyana fatansa na cewa Asma’u za ta jagoranci sauran shugabannin cibiyar Kungiyar ta yadda za ta bar abubuwan da ba za a iya mantawa da su ba a sauran sassan da suka rage a aikinta, sannan ya bukace ta da ta mai da hankali da yin azama yayin gudanar da harkokin ta.

Tun da farko, shugabar kungiyar ta NUJ ta Kaduna, Kwamared Asma’u Yawo Halilu wadda ta bayyana wasu nasarorin da Kungiyar ta samu a cikin watanni biyar da suka gabata, ya danganta gagarumin ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu ga gagarumin goyon bayan da take samu daga mambobin kungiyar da abokan huldar ta.

Ta ci gaba da cewa, sun aiwatar da shirin horarwa don inganta ƙwararrun mambobi tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin jama’a na ci gaba da gudana a jihar.

Ta ce “duk waɗannan nasarorin, an cimma musu ne saboda tallafin da muka samu daga abokan tarayya, masu girma membobinmu kuma tabbas saboda mu ma mun mai da hankali kuma muna da hangen nesa.”

“A yau jagoranmu, Dan Jarida na daya a Najeriya, Kwamared Chris Isiguzo zai kaddamar da dukkan wadannan ayyukan. Namu ne Ina muku barka da zuwa Jihar Kaduna a wannan wata na musamman.”

“Bari kuma in yi amfani da wannan dama don tabbatar wa mambobinmu cewa jindadin ku shi ne mafificin mu. Kamar yadda kuka sani, sana’ar mu tana buƙatar ci gaba da horarwa. Dole ne mu kasance masu horo kafin mu iya sanar da wasu.”- Acewar Asma’u

Tsohon Shugaban Kungiyar, Kwamared Yunusa Aliyu, wanda ya yi magana a madadin tsoffin shugabannin Kungiyar, ya yabawa Kwamared Asma’u Halilu inda ya bayyana ta a matsayin mace mai kamar maza wacce ta ke kokarin ganin ta daidaita al’amura tare dawo da martabar Kungiyar ta hanyar kwazonta dana abokan aikinta wanda suke nuna jajircewa wajen gudanar da wannan aiki.

Babban abin da ya fi daukar hankali a taron shi ne kaddamar da ayyukan da Comrade Asma’u ta jagoranta ta EXCO da shugaban kungiyar ya gudanar wanda suka hada da sashen wasanni, samar Sabon Ofishin Kungiyar Wakilai, gyaran cibiyar da sauran abubuwa.

Leave a Reply