NLC Kaduna Ta Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman A Masallacin Juma’a Na SMC

0
352

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A CI gaba da shirye-shiryen gudanar da harkokin bukin ranar ma’aikata ta shekarar 2022 da ta ke yi, kungiyar kwadago ta kasa (NLC), reshen jihar Kaduna a ranar Juma’a 29 ga Afrilu, 2022 ta gudanar da addu’o’in godiya ta musamman a Masallacin Kwalejin tunawa da Sardauna, (SMC) Juma’a dake Kaduna.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan idar da Sallar da addu’o’in, Shugaban Kungiyar reshen Jihar Kaduna, Kwamared Ayuba Magaji Suleman, ya bayyana cewa sun ga ya dace su shirya addu’o’i na musamman da kuma neman taimakon Allah wajen gudanar da ayyukansu domin samun nasarar gudanar da bukukuwan da za a gudanar a ranar Lahadi mai zuwa.

Kwamared Suleman ya kara da cewa, tun kafin yanzu, Kungiyar ta fara gudanar da ayyukan tare da gabatar da yin godiya a coci a ranar Lahadi 24 ga Afrilu, 2022 a St. Augustine’s Catholic Church, Kaduna, kana ta gudanar da taron karawa juna sani a ranar Laraba domin wayar da kan jama’a game da ranar Mayu.

Ya ce “akwai bukatar mu saka Allah a cikin ayyukanmu, shi ya sa muka zo wannan masallacin Juma’a na Sheikh Saba dake SMC domin yi wa ma’aikata addu’a, mu yi addu’o’in da za a yi biki ba tare da wata matsala ba kuma da yin addu’ar samun nasarar gwagwarmaya.”

Shugaban na Jiha, ya ci gaba da bayanin cewa, batun Kungiyar na shiga harkokin siyasa, wannan manufar sakatariyar Kungiyar ta kasa ne da ta sanya mambobinta su shiga harkokin siyasa domin shugabancin kasa na da tsarin siyasar da ke bin diddigin al’amura don haka ta umurci daukacin mambobin kungiyar a matakin Jiha da yin haka.

“A jiya shugabannin Kungiyar na jihar sun halarci wani taron tattaunawa da shugabancinta na kasa a bisa irin shirye-shiryen ganin ma’aikata sun shiga harkokin siyasa a wannan zagaye na siyasa na 2023, kuma a shirye muke a kowane lokaci domin mun gamsu cewa abu ne mai kyau da domin za a iya samar da shugabanni ne kawai ta hanyar gudanar da zabe, don haka za mu fara aiwatar da tsarin tun daga farko har zuwa karshe.

“Kuma abin da muke so a matsayinmu na ma’aikata shi ne bukata, kuma za mu hada kan wadannan ‘yan siyasa don tabbatar da sun cika mana alkawurra dangane da bukatunmu saboda ba ma so mu fuskanci abin da muka samu a shekarun baya, wanda bayan mun zabi mutane kuma sai su dawo su zama makiyanmu su hana mu albashi, hana mu mafi karancin albashi, hana mu alawus, su hana mu abubuwa da yawa.” – A cewarsa.

A karshe, Kwamared Ayuba Magaji Suleman, ya yi kira ga ma’aikata da su jajirce da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukansu domin ci gaban rayuwarsu, don da haka ake ganin darajar rayuwarsu ta ci gaba.

Leave a Reply