Yadda Garin Katari Zuwa Rijana Ya Gagari Jami’an Tsaron Najeriya

0
577

Daga; Rabo Haladu, Kaduna.

MATSALAR tsaro a hanyar Abuja zuwa Kaduna na sake zama babbar barazana musamman a wannan lokaci da hanyar da galibin mutane suka runguma na bin Jirgin kasa domin neman tsira ke fuskantar wata sabuwar barazanar.

Fasinjoji na rububbin bin jirgin kasa saboda kaucewa hare-haren ‘yan bindiga a hanayar Abuja zuwa Kaduna

Harin da ‘yan bindiga suka kai ranar Litinin da daddare tare da garkuwa da Jama’a da dama a Jirgin kasa da ke hanyar Kaduna daga Abuja ya sake jefa tsoro a zukatan matafiya.

Galibin ‘yan kasar na cewa kusan babu zaɓin da ya rage garesu ganin cewa hanyar mota ba tsaro ga na jirgin kasa ma na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.

Garuruwan Katari zuwa Rijana sun kasance yankin da ‘yan bindiga ke yawaita cin karensu babu babbaka kan matafiya, inda ko a wannan lokaci ana suka tare jirgin kasa tare da buɗewa fasinjoji wuta.

Mutane da ake cewa sun rasu sun kai bakwai sannan sama da 22 sun jikkata, akwai kuma da dama da ba a ji duriyarsu ba tun bayan hari kan jirgin da ke dauke da fasinjoji 970.

Harin ya zo ne kwana guda bayan harin da ‘yan bindiga suka kai tashar jirgin sama da ke Kaduna.

Shin tsaron hanyar Kaduna zuwa Abuja ya gagari gwamnatin Buhari ne?
Wannan yanayi ya dimauta ‘yan Najeriya da dama musamman ganin yadda matsalar tsaro ke neman hana su zirga-zirga da bin hanyar da kasance wajibi ga duk mutumin da ke son zuwa yankunan Arewa maso yamma da Arewa maso gabashin kasar daga Abuja.

Masana dai na ganin matsalar tsaro a Najeriya na ci gaba da gaggara hukumomi ganin cewa a kodayaushe da an soma tunanin sauki sai abubuwa su sake rincabewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here