Tinubu Ba zai musuluntar da Najeriya ba – Masari

0
226

Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya bayyana ikirarin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, zai musuluntar da Najeriya idan aka zaɓe shi shugaban kasa a 2023 a matsayin batu mara tushe.

Da yake magana a ranar talata a wani taron da ƙungiyar Kiristocin Arewa ‘yan siyasa a lokacin da suka tarɓi uwargidan Tinubu, Sanata Remi Tinubu, a kaduna, Masari ya ce ko makaho ne zai zaɓi Tinubu, domin ya fi ɗaukacin ‘yan takarar shugaban ƙasa.

Masari ya bayyana jihar Legas a matsayin ƙaramar Najeriya, inda ya ce Kiristoci da Musulmi da ma arna duk suna zaune a Legas amma duk da haka Tinubu yayi kokarin kawo cigaba a jihar.

“Ba wani tushe balle makama kan tsoron cewa Tinubu zai musuluntar da Najeriya, ba gaskiya bane, shin Buhari ya musulunta Najeriya bayan shekara bakwai yana mulki?

“Shin Obasanjo ya Kiristantar Najeriya bayan shekaru takwas yana mulki?

“Shin Jonathan ya mayar da Najeriya kasar Kirista bayan shekaru shida yana mulki? Inji shi.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babbar matsalar ƙasar nan, ita ce siyasa da baƙin ciki.

Ya bayyana cewa idan matasa maza da mata za su taru domin wani aiki na bai ɗaya ba tare da baƙin ciki ba, za a samu cigaba a ƙasa.

“Tarihi zai maimaita kansa,” a lokacin mulkin soja ƙarƙashin Janar Ibrahim Babangida ya koma mulkin farar hula, an yi zaɓe tsakanin MKO Abiola na SDP da Alhaji Bashir Tofa NRC, abokin takarar Abiola musulmi ne, tikitin takarar musulmi da musulmi ne ya lashe zaɓen, Tofa, wanda ya zaɓi abokin takararsa Kirista ya sha kaye a zaɓen. Don haka Tinubu ne zai ci zaɓe,” inji Ganduje

Shi ma da yake jawabi, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-rufai, ya ce gwamnonin APC na arewa sun yanke shawarar marawa ɗan takarar shugaban ƙasa a kudancin ƙasar baya “domin haɗin kai, daidaito da adalci a ƙasar nan.

“Bayan mulkin shugaba Buhari, ya dace fadar shugaban ƙasa ta tafi kudu. Kuma mun yi taro a Katsina a gaban Gwamna Aminu Bello Masari inda ya ce a cikin dukkan masu neman takarar shugaban ƙasa mu mara wa Ahmed Tinubu saboda irin nasarorin da ya samu a lokacin da yake gwamnan Legas.”

KU KUMA KARANTA:Zan yi adalci ga kowa, alƙawarin Tinubu ga ‘yan Najeriya

Sanata Oluremi Tinubu, ta ce mijinta ba zai yiwa ‘yan Najeriya riƙon sakainar kashi ba idan har aka zaɓe shi a karagar mulki, inda ta bayyana shi a matsayin ma’aikacin aiki kuma mutum ne mai “cike da hankali”.

Shugaban ƙungiyar matasan Kiristocin arewa, Mista Isaac Abra, ya ce Tinubu ne ya fi kowa cancantar tsayawa takarar shugaban ƙasa saboda abubuwan da ya yi a baya.

Leave a Reply