2024: Jami’an ‘yansanda 140 ne suka mutu a Abuja
Wasu daga cikin iyalan mamatan sun riga sun karbi hakkokinsu da sauran tallafi kamar yadda babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya ba da umarni.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta yi asarar jami’anta 140 da ke aiki a birnin tarayya, Abuja, a shekarar 2024 da ta gabata.
A sanarwar karshen shekarar da rundunar ‘yan sandan Abuja ta fitar game da nasarorin da ta samu tun daga watan Janairu zuwa Disemban 2024, kwamishinan ‘yan sanda, Olatunji Disu ya ce wasu daga cikin zaratan jami’ansa 140 sun mutu sakamakon arangama da ‘yan shi’a da wasu nau’ukan tarzoma da cutar hawan jini a birnin Abuja a 2024.
KU KUMA KARANTA:‘Yan sanda sun kama wani da ya caka wa ’yar shekara 8 almakashi a gabanta
Ya kuma bayyana cewa wasu jami’an ‘yan sandan sun mutu a cikin baccinsu a yayin da wasu suka yanke jiki suka fadi a bakin aiki.
A cewarsa, wasu daga cikin iyalan mamatan sun riga sun karbi hakkokinsu da sauran tallafi kamar yadda babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya bada umarni.