2023: Yadda Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa

2
446

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar ne ya bayyana haka da misalin ƙarfe 4:10 na safiyar Laraba.Ya ce Tinubu ya samu ƙuri’u 8,794,726 inda ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya sami ƙuri’u 6,984,520, yayin da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya sami 6,101,533, sai kuma Rabi’u Kwankwaso na NNPP ya sami ƙuri’u 1,496,687.

Sanarwar wacce aka yi a cibiyar tattara bayanai ta ƙasa da ke Abuja, ta yi nuni da kawo karshen ayyukan tattara sakamakon da aka fara a ranar Lahadi.Da yake bayyana sakamakon ƙarshe, Shugaban INEC ya ce Tinubu da jam’iyyar APC sun cika sharuɗɗan tsarin mulki.

Yakubu ya ce za a ba Tinubu da abokin takararsa Sanata Kashim Shettima takardar shaidar cin zaɓe da ƙarfe 3 na yamma ranar yau Laraba.

2 COMMENTS

Leave a Reply