2023: Mun shirya yaƙi da sayen ƙuri’u- shugaban INEC

1
430

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, (INEC) ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hana sayen ƙuri’u a babban zaɓen 2023.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wani taron yini da masu ruwa da tsaki suka yi, na magance tasirin kuɗi a zaɓen 2023 da aka yi ranar Litinin a Abuja.

Farfesa Yakubu ya ce a matsayin hukumar INEC, ba ta yi tunanin cewa zai yi sauƙi wajen kawar da munanan tasirin da kuɗi ke da shi a zaɓen ba, amma duk da haka ta ƙuduri aniyar shawo kan lamarin.

“Mun fahimci cewa, shirin na yau, ba zai yi daɗi ga mutanen da ba za su jajirce wajen ci gaban tsarin zaɓenmu da kuma tabbatar da dimokuradiyyar mu ba.

“Muna sa ran mu ji ta bakin su, za a sami matsin lamba na ɓoye da na bayyane, ayyukan da ba su dace ba har ma da barazanar waɗannan buƙatu.

KU KUMA KARANTA:‘Yan siyasa na sayen katin zaɓe -INEC

“Ina so in sake jaddada cewa biyayyarmu ga Najeriya ce kuma biyayyarmu ga ‘yan Najeriya ne, Mun himmatu wajen yin aiki tare da hukumomin haɗin gwiwa don ganin cewa wannan shiri ya yi nasara a zaɓen 2023 da ma bayansa.

“Hukumar tana sane da cewa tanade-tanaden doka da ayyukan hukumomin suna da matukar muhimmanci amma ba za su kai ga kawar da cutar sankara ta cin hanci da rashawa gaba ɗaya a zabenmu ba,” inji shi.

Shugaban na INEC ya ƙara da cewa: “Ayyukan haɗaka na ‘yan ƙasa na da matukar muhimmanci, dole ne ‘yan ƙasa su yi watsi da ƙwazo don murƙushe tsarin sayar da ƙuri’unsu.

“Har ila yau, dole ne su taka rawa yadda ya kamata wajen daƙile mummunar amfani da kuɗi a harkokin zaɓenmu gaba ɗaya ta hanyar kai rahoto ga INEC da sauran hukumomi.

“Bugu da ƙari, ya kamata kungiyoyin farar hula su mayar da wannan wani babban shiri na dukkan ayyukansu na sa idon kafin zaɓen da kuma lokacin zaɓen.

“Cibiyoyin kuɗi, ƙungiyoyin addini, cibiyoyin gargajiya, kafofin watsa labarai, ƙungiyoyin jama’a, da sauransu, dole ne ‘yan ƙasa su shiga cikin wannan yaƙin” in ji shi.

1 COMMENT

Leave a Reply