2023: Buhari baya goyon bayan ko wane ɗan takara, Lai Mohammed ga El-Rufa’i

0
493

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari baya goyon bayan kowane ɗan takarar shugaban ƙasa, a maimakon haka ya jajirce wajen ganin an gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, in ji ministan yaɗa labarai Lai Mohammed kamar yadda ya shaida a ranar Laraba.

Lai Mohammed ya shaida haka ne a Abuja a karshen taron majalisar zartarwa ta tarayya a lokacin da ministan amsa tambayar wani ɗan jarida da ya nemi ya mayar da martani kan ikirarin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai na cewa wasu jami’an fadar shugaban ƙasa ba sa son Bola Tinubu, ɗan takarar jam’iyya mai mulki ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da za ayi a wannan watan.

“Abu ɗaya da zan iya tabbatar muku shi ne, ko mene ne, wannan gwamnatin ta mayar da hankali ne, wajen tabbatar da sahihin zaɓe. Amma ina ganin a wannan gwamnati, babban mutum mai muhimmanci shi ne shugaban ƙasa kuma ina ganin ya nuna ta baki da kuma cewa ya sadaukar da kai wajen gudanar da sahihin zaɓe da gaskiya,” inji shi.

KU KUMA KARANTA:PDP ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa Shugaba Buhari a Kano, ta ɗora laifin kan Tinubu da Ganduje

“Kuma zaɓuka na gaskiya, ‘yanci, sahihanci yana nufin rashin fifita kowa, ba cutar da kowa ba, kuma duk inda ya je sai ya bayyana hakan a fili, ko a kwanan baya a lokacin da ya ke Daura ya fadi haka.”

Ga dukkan alamu bayanin na Lai Mohammed ya ci karo da kalaman da fadar shugaban ƙasa ta yi a baya na cewa shugaba Buhari ya jajirce wajen goyon bayan Tinubu da sauran ‘yan takarar APC a babban zaɓe.

A ranar Laraba, Ministan yaɗa labaran ya ƙara da cewa bai da masaniyar cewa wani a fadar shugaban ƙasa yana aiki akan manufar Tinubu.

“Idan akwai wanda ke adawa da ɗan takara, ba mu sani ba a hukumance,” in ji Lai Mohammed.

Da safiyar ranar Laraba ne gwamna El-Rufai ya furta kalaman ca ya ke cewa wasu jami’an fadar shugaban ƙasa ba sa son Tinubu ya ci zaɓen shugaban ƙasa.

Leave a Reply