2023: Bamu yarda a yi kamfen da waƙoƙin Fela ba- Iyalan Fela

0
514

Daga Maryam Sulaiman

Iyalan marigayi Fela Anikulapo Kuti sun fitar da wata sanarwa inda suka nuna rashin yardarsu da yin amfani da wakar Fela wajen yakin neman zabe.

Jam’iyya mai mulki ta APC ta yi amfani da shahararriyar wakar Fela mai suna “Eko Ile” a matsayin wani salo, na yakin neman zaben shugaban ƙasa na 2023, lamarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin masu amfani da yanar gizo da suka yi hasashen cewa iyalan Kuti suna goyon bayan jam’iyyar APC.

A wani sako da Femi Kuti ya fitar a shafinsa na sada zumunta da muhawara, ya bayyana cewa matakin da jam’iyyar APC ta ɗauka ba tare da izinin su bane, kuma dangin Kuti ba sa bin wata jam’iyyar siyasa.

A cewar sa; “Rashin yarda da sanarwa da amfani ba tare da izini ba, mu masu kula da kadarorin Fela Anikulapo-Kuti ne muka fitar da wannan sanarwar.

“Muna so mu bayyana a nan don a sani, cewa ba a nemi izinin mu ba don amfani da waƙar Fela, Eko Ile, a cikin yaƙin neman zaɓe na APC na kafofin watsa labarun da ke yawo a halin yanzu.

“Ba ma saka wakar Fela a duk wani kamfen na siyasa a gida ko waje, kuma mun zaɓi mu kasance tsaka tsaki, mu na yi wa dukkan ‘yan takara fatan alheri, muna neman a kiyaye dokokin Tarayyar Najeriya da kuma mutunta ‘yancin mallakar fasaha” inji iyalan Fela.

Leave a Reply