Ɗan fashin mota ya kashe jami’in kwastam a Kebbi

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) reshen jihar Kebbi, a ranar Lahadin da ta gabata ta tabbatar da kisan wani ma’aikacinta mai suna Aminu Abdullahi da wani da ake zargin mai safarar motoci ya yi a ƙaramar hukumar Yauri ta jihar.

Kakakin hukumar, ASC Mubarak Mustapha, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi.

Ya ce: “Hukumar NSC reshen jihar Kebbi, ta jajantawa iyalan jami’in kwastam, Aminu Abdullahi, wanda wani da ake zargin ɗan safarar mota ne ya kashe a lokacin da yake bakin aiki.

“Lamarin ya faru ne a ranar 13 ga watan Yuli, da misalin ƙarfe 4:00 na safe, inda wata mota ƙirar Toyota Corolla ta shekarar 2015 mai lamba: 2TBURHE3FC456204 ta kutsa cikin mamacin da ke kan hanyar Tamac, ƙaramar hukumar Yauri ta jihar”.

Ya ce an garzaya da jami’in zuwa babban asibitin garin Yauri domin samun kulawar gaggawa bayan an kai masa ɗaukin gaggawa.

“Daga baya an ɗauke shi zuwa Asibitin Orthopedic na Wamakko da ke ƙaramar hukumar Wamakko ta Jihar Sakkwato.

“Abin takaici, ya rasu a wannan safiya bayan ya amsa magani a cikin dare,” in ji shi.

Malam Mubarak ya yi addu’ar Allah ya jiƙan mamacin ya kuma baiwa iyalansa haƙurin jure rashin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan Majalisu sun nemi kawo ƙarshen kashe-kashe a Zamfara

Kakakin ya ce, an kama ɗaya mai suna Abdulwasiu Salawudeen, wanda ke tuƙa motar, kuma an kai shi hedikwatar rundunar domin ci gaba da bincike.

A halin da ake ciki, hukumar ta ce ta shirya fareti a karon farko cikin shekaru uku domin ƙara ƙwarin gwiwar jami’anta da mazajensu.

“Dalili na faretin shi ne ƙarfafa gwiwa, dasa ladabtarwa, ɗaure jami’an tsaro daidai gwargwado da aiwatar da muhimman ayyukan hukumar NCS na samar da kuɗaɗen shiga, daƙile fasa-ƙwauri, sauƙaƙa harkokin kasuwanci, samar da tsaro da kuma inganta dangantakar kwastam ga al’ummomin da suka karɓi bakuncinsu.

Ya ƙara da cewa “Kwamantin yankin na rundunar, Dakta Ben Oramalugo ya jaddada buƙatar jami’an su kasance masu kula da ‘yan’uwansu kuma su riƙa ganin juna a matsayin ‘yan uwa sanye da kayan aiki, sannan kuma su taimaka wa juna da hankali da ƙarfafa gwiwa,” in ji shi.


Comments

3 responses to “Ɗan fashin mota ya kashe jami’in kwastam a Kebbi”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Ɗan fashin mota ya kashe jami’in kwastam a Kebbi […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Ɗan fashin mota ya kashe jami’in kwastam a Kebbi […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *