Ɗalibin jami’a ya rasu yana tsaka da rubuta jarrabawar ƙarshe a jami’ar Gombe

0
258

Wani ɗalibin jami’ar jihar Gombe da ke zangon karatu na ƙarshe mai suna Abubakar Muhammad, ya rasu yayin da yake tsaka da rubuta jarrabawar kammala makarantar.

Ɗalibin dai na karatu ne a sashen koyon aikin Akanta na jami’ar.

Wani abokin karatun marigayin ya bayyanawa wakilinmu cewa marigayin ya zo ɗakin rubuta jarrabawa a ranar sai rashin lafiya ta kama shi inda nan take aka garzaya da shi zuwa cibiyar lafiya ta jami’ar dan duba lafiyarsa.

Sai dai a cewar majiyar, jikin ɗalibin ya tsananta, amma kafin nan rai ya yi halinsa, inda aka wuce da shi ɗakin adana gawarwaki a asibiti.

KU KUMA KARANTA: Amarya ta rasu ranar ɗaurin auren ta a Oyo

“Ya rasu a cibiyar lafiya ta jami’ar sannan daga bisani mataimakin shugaban sashen tsaro na jami’ar ya jagoranci ɗaukar gawar zuwa ɗakin adana gawarwaki na asibitin ƙwararru na Jihar Gombe tare da wasu abokansa da kuma wasu jami’an jami’ar,” in ji ɗalibin.

Da wakilinmu ya tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar, Mohammed Abubakar, ya tabbatar da rasuwar ɗalibin.

Sai dai ya ce dama ɗalibin ba shi da lafiya a ranar tun kafin shigarsa ɗakin rubuta jarrabawar.

Leave a Reply