Ɗaliba ta tayar da gobara a makaranta saboda an ƙwace mata waya, 19 sun mutu

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wata ɗaliba da aka ƙwace wa waya a makaranta ta tayar da gagarumar gobara a ɗakin kwanan ‘yan uwanta ɗalibai a wata makaranta a Guyana, in ji hukumomi.

Mutane goma sha tara ne yawanci ɗalibai mata suka rasu a gobarar, a ƙasar ta Latin Amurka a cikin daren Litinin.

Ɗakin kwanan an ce yana kulle kuma duk tagoginsa na rufe, abin da ya hana ɗaliban samun damar tserewa ke nan.

KU KUMA KARANTA: Gobara ta tashi a wani ɓangare a fadar Ooni

Ɗalibar ‘yar shekara goma sha ita ma wutar da ƙona ta inda yanzu take kwance a asibiti kuma rahotanni sun ce ta amsa cewa ita tayar da wutar.

Hukumomi na neman shawara kan ko za su tuhume ta da laifin tayar da gobarar, kamar yadda wani ya sheda wa kamfanin dillancin labaran AFP.

Rahotanni sun ce gobarar ta fara ne daga wurin banɗaki sannan ta kama ginin gaba ɗaya wanda na katako ne da ke ɗauke da ɗalibai 57 a lokacin.

Waɗanda suka tsira da ransu a gobarar a garin Mahdia na tsakiyar kasar sun ce ihu da kururuwar da suka ji a cikin dare ne ya tashe su.

Bayanai sun nuna cewa yarinyar ta yi barazanar aikata abin bayan da aka hukunta ta saboda tana alaƙa da wani namiji babba wanda ya girme ta.

‘Yan kwana-kwana sun riƙa fasa tagogin ginin ne kafin su iya cetar waɗanda suka tsira da rai.

Wasu ɗaliban sun ƙone sosai ta yadda sai an yi gwajin ƙwayoyin halitta kafin a iya gane gawarwakinsu.

Shugaba Irfaan Ali da farko ya bayyana lamarin a matsayin babban bala’i.


Comments

One response to “Ɗaliba ta tayar da gobara a makaranta saboda an ƙwace mata waya, 19 sun mutu”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Ɗaliba ta tayar da gobara a makaranta saboda an ƙwace mata waya, 19 sun mutu […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *