Ƙungiyar USAID ce ta ɗauki nauyin ƙungiyar Boko Haram – Ɗan Majalisar Dokokin Amurka
Daga Ibraheem El-Tafseer
Ɗan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi iƙirarin cewa hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) ce ke tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.
Perry, ɗan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan iƙirarin ne a yayin da ake gudanar da taron sauraron ƙararrakin zaɓe na ƙaramin kwamiti kan isar da ingancin gwamnati a ranar Alhamis.
Ƙungiyar Boko Haram, wacce aka fi sani da Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, ƙungiya ce ta ‘yan ta’adda da ta ayyana kanta a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kuma tana aiki a kasashen Chadi, Nijar, arewacin Kamaru da kuma Mali.
Ƙungiyar ta shafe sama da shekaru 15 tana tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta kashe dubun-dubatar mutane, a hare-haren da ake kai wa ‘yansanda, da sojoji da fararen hula.
KU KUMA KARANTA:MƊD ta ƙaddamar da bugu biyu na ‘Muryoyin Sahel’
Hare-haren Boko Haram ya yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000 tare da raba miliyan 2.3 da muhallansu da kuma haddasa matsalar abinci da yunwa a yankin.
Ana ware kuɗi dala miliyan 697 a duk shekara, tare da jigilar kuɗaɗe na musamman a ƙungiyoyin ISIS, Al-Qaeda, Boko Haram, ISIS Khorasan, sansanonin horar da ‘yan ta’adda. Wannan shi ne abin da ake bayarwa, ”in ji Perry.
Perry ya ƙara da cewa hukumar ta USAID ta bayar da dala miliyan 136 don gina makarantu 120 a Pakistan, yana mai zargin cewa babu “shaida” na gina makarantun.
“Kuna ɗaukar nauyin ta’addanci ta hanun USAID. Kuma ba Afganistan kaɗai ba, saboda Pakistan na kusa da maƙwabta.