Ƙungiyar Marubuta Alƙalam da ke Kaduna ta bayyana cewa za ta shirya taron tunawa da uban ƙungiyar kuma gwarzon ɗan kishin ƙasa ɗin nan, Alhaji Mahmoon Baba-Ahmed, wanda Allah ya yi wa rasuwa shekaru biyar da su ka gabata.
Shugabar ƙungiyar, Hajiya Halima Abdullahi K/Mashi, ta bayyana a cikin wata takarda ga manema labarai cewa za a yi taron a Gidan Arewa da ke Kaduna a ranar Alhamis, 9 ga Fabrairu, 2023, wadda ta yi daidai da shekaru biyar cur da rasuwar marubucin.
Alhaji Mahmoon ya rasu ne a Kaduna a ranar Alhamis, 9 ga Fabrairu, 2018, ya na da shekaru 77 a duniya.
Mahmoon Baba-Ahmed sanannen ɗan jarida ne kuma marubuci wanda ya yi fice a aikin rediyo a matsayin wakilin gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna a jihohi da dama. Daga bisani ya riƙe muƙamai da su ka haɗa da Shugaban gidan Rediyon Kano da Manajan Daraktan Hukumar Yaɗa Labarai ta Jihar Kaduna (KSMC).
Haka kuma ya kasance mai sharhi kan al’amurran yau da kullum a filayen musamman da aka ware masa a jaridu da su ka haɗa da Triumph, Blueprint da Aminiya, da kuma gidajen talabijin na DITV da Liberty da gidan rediyo na Alheri da na Liberty.
Marigayi Mahmoon ya rubuta littattafan adabi guda shida a rayuwar sa waɗanda su ka haɗa da littafin waƙe mai suna ‘Ɗan Hausa’, da littattafan wasan kwaikwayo guda biyu (‘Uwani Reza’ da ”Yar Halas’), da fassarar littattafai uku na mashahurin marubucin nan na ƙasar Ingila, wato William Shakespeare.
KU KUMA KARANTA:Ina burin a tuna ni a marubucin dake nusar da shugabanni – Gimba
Littattafan Shakespeare da ya fassara su ne: ‘Macbeth’ (‘Makau’), ‘Julius Caesar’ (‘Jarmai Ziza’), da ‘Romeo and Juliet’ (‘Habiba Ta Habibu’).
Takardar sanarwar ta ce ɗaya daga cikin abubuwan ban-sha’awa da za a gudanar a taron shi ne gabatar da littafin ƙarshe da Mahmoon ya rubuta, wato ‘Habiba Ta Habibu’, wanda shi kaɗai ne marigayin bai samu bugawa ba har ya rasu, amma an buga shi a bana.
Hajiya Halima ta kuma bayyana cewa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, shi ne babban baƙo na musamman a taron, yayin da Shugaban gidan talabijin da rediyo na Liberty, Dakta Ahmed Tijjani Ramalan, shi ne shugaban taron.
Bugu da ƙari, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, zai kasance uban taron, yayin da tsohon Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya, Mai Shari’a Umaru Abdullahi (Walin Hausa), shi ne babban baƙo na musamman.
Ta ce Shugaban Shiyyar Kaduna ta hukumar Gidan Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), Alhaji Buhari Auwalu, shi ne babban baƙo mai jawabi, sannan babban malami a Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Adamu Ibrahim Malumfashi, zai yi sharhi kan littattafan marigayin.
A cewar shugabar ƙungiyar, manufar taron ita ce a tuno da muhimman ayyukan kishin ƙasa da Alhaji Mahmoon yayi, tare da ƙara kwaɗaita wa jama’a muhimmancin sambarka ga magabatan mu da su ka ba da gudunmawa ga cigaban ƙasa ta hanyoyin da Allah hore masu.
Ta ce za kuma a yi amfani da wannan damar a karrama wasu ‘ya’yan ƙungiyar ta Alƙalam waɗanda su ka riga mu gidan gaskiya.