Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci gwamnati ta janye ƙarin farashin mai

0
52
Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci gwamnati ta janye ƙarin farashin mai

Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci gwamnati ta janye ƙarin farashin mai

An wayi gari a ranar talata a sassan ƙasar da ƙarin farashin litar mai inda ake sayar da shi naira 855, zuwa 897 daga naira 568 akan kowace lita.

Rahotanni sun ce kamfanin NNPC ne ya ƙara farashin.

Sai dai cikin wata takataitacciyar sanarwa da ta wallafa a shafukan sada zumunta a yammacin Talata, ƙungiyar ta NLC ta yi ƙira ga gwamnati da ta mayar da farashin yadda yake a da.

KU KUMA KARANTA: Mun gano haramtattun hanyoyin da ake satar man fetur a Najeriya – NNPC

“Muna ƙira da a janye ƙarin farashin mai da aka yi a sassan ƙasar ba da ɓata lokaci ba.” Sanarwar ta ce.

Ƙarin farashin na zuwa ne yayin da ake fama da matsalar karancin mai a sassan kasar.

Kazalika ƙarin na zuwa ne kwanaki biyu bayan da kamfanin NNPC ya yi korafin cewa ana bin sa maƙudan kuɗaɗe da yawansa ya kai dala biliyan 6 na kuɗin masu shigo da mai.

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta musanta ba kamfanin na NNPC umarnin ya ƙara farashin na litar mai.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Ministan Mai, Sanata Heineken Lokpobiri ya nesanta gwamnatin da ba da umarnin ƙarin “kamar yadda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.”

“Muna masu Allah wadai da wannan iƙirari da ba shi da tushe, wanda yunƙuri ne na fusata jama’a.” sanawar ta ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here