Ƙididdigar watannin shekara a ƙasar Hausa
Daga Yusuf Alhaji Lawan
Daga cikin ɗabi’un Hausawa har da yin aron kalmomin da ba su da su a harshen su, su yi musu kwaskwarima su mayar da su nasu. Wannan bai taƙaita ga kalmomi ba, ya kai har ga wasu ginshiƙai da ke da alaƙa da zamantakewa ta yau da kullum.
Daga manyan harsunan duniya da Hausawa suka fara haduwa da su akwai Larabci, wanda daga tasirin wannan har da kasancewar mafi yawan Hausawa sun rungumi musulunci a matsayin addini. Shi kuma addinin musulunci an saukar da shi ne da harshen Larabci, kuma duk wanda zai yi addinin, yana da buƙatar samun kusanci da harshen larabci.
Wannan yasa aka samu kalmomin Larabci da yawa da harshen Hausa ta ara, wanda wasu na ganin cewa kalmomin Larabci a harshen Hausa sun ɗauki kaso mai tsoka.
Wasu kalmomin da aka aro, ana amfani dasu a yadda suke a asalin harshen larabcin, wasu kuma an jirkita su kaɗan, sai ake amfani da su akan asalin ma’anoninsu, amma wasu kuma an ɗauke su aka ba su ma’ana daban daga asalin yadda suke a tushe.
Ba a iya Larabci Hausawa suka ari kalmomi ba, har da turanci da ma wasu harsuna da ke kusa da su musamman akan sunayen abubuwa da ba su da su a wajen su, ko wasu al’amura da suke baƙi a wajen su.
A abinda ya shafi ƙidaya na watannin shekara, tsawon lokaci Hausawa na amfani da watannin musulunci, amma ba sa kiran su da asalin sunayen su a harshen larabci, sun yi musu kwaskwarima da basu wasu sunaye, suna kiransu da yadda suka ga zai fi musu sauƙi.
Kuma duk harkoki da suka shafi sanya rana domin biki ko wasu tarurruka, to suna yi ne da waɗannan sunayen watannin. Hatta abin da ya shafi al’adunsu sun ta’allaƙa da lissafin waɗannan watannin ne.
KU KUMA KARANTA: Amfani Da Hoton Wani A Shafinka Na Sada Zumunta: Dacewa ko akasin haka?, daga Yusuf Alhaji Lawan
Sai dai kuma ba a nan gizo ke saƙa ba. Yanzu sunayen waɗannan watannin sun fara ɓacewa a tsakanin Hausawa da ma masu amfani da harshen Hausa wajen sadarwa.
Bibiyar ƙidayar su na zama aiki da ba kowa ke iya bi ba, wasu abubuwa na al’ada da aka jingina da su sun fara zama tarihi, wasu kuma na kuɓucewa ba tare da lura ba.
Zamani ya sanya yanzu da yawa sun koma amfani da watannin Boko, kuma su ɗin ma maimakon a ambace su da Hausa sai ake ambaton su da turanci.
To a nan, za mu ambaci sunayen watannin larabci da yadda Hausawa suke ambatar su domin amfanin masu karatu.
1. Muharram – Watan Shara/ watan Cika-ciki/ watan Jela
2. Safar – Watan Zafi
3. Rabi’ul Auwal – Watan Maulidi
4. Rabi’us Thani – Tagwai na Farko
5. Jimada Auwal – Tagwai na Biyu/Ƙarshe
6. Jimada Thani – Gambon wata
7. Rajab – Watan Azumin Tsofi
8. Sha’aban – Watan Sallar Tsofi
9. Ramadan – Watan Azumin duk Gari
10. Shawwal – Watan Ƙaramar Sallah
11. Zulƙida – Watan Bawa
12. Zulhajji – Watan Babbar Sallah
Wata rana idan Allah ya ba da iko, za mu yi rubutu akan abin da ya shafi kowanne daga waɗannan watannin da abubuwa da suke ƙumshe da su a wajen Hausawa domin ƙara fahimtarsu. To yana da kyau mu koma kan tsarin da muka gada daga iyaye da kakanni, mu riƙe harshe da al’adun mu domin ci gaban mu gaba ɗaya.
Yusuf Alhaji Lawan ya rubuta daga Anguwar Hausawa Asibiti, Garin Potiskum, Jihar Yobe. Za’a iya tuntubar sa ta nasidi30@gmail.com.