Ƙasar Rasha ta kai farmaki mafi girma da jirage marasa matuƙa Ukraine

0
29
Ƙasar Rasha ta kai farmaki mafi girma da jirage marasa matuƙa Ukraine

Ƙasar Rasha ta kai farmaki mafi girma da jirage marasa matuƙa Ukraine

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce Rasha ta harba makaman mizal guda 120 da jirage marasa matuƙa 90, a wani farmaki mai girma da ta kai a faɗin Ukraine inda ta auna wuraren samar da makamashin ta.

Jiya Lahadi, Zelensky ya ce, Rasha ta kai farmaki da samfirin jirage marasa matuƙa daban daban cikin su har da samfirin Shahed, makaman mizal masu sarrafa kansu da makamai masu cin dogon zango.

Ya ce na’urorin kare hare haren saman Ukraine sun kakkaɓo jirage marasa matuka 140.

Tun bayan da ta fara mamayar ta gadan gadan a kasar dake makwabtaka da ita a watan Fabrairun 2022, Rasha tayi ta auna cibiyoyin samar da makamshin Ukraine, lamarin da ya sa ƙasar ta tsinci kanta cikin yanayin gaggawa wanda ya jefa ƙasar baki ɗaya cikin duhu bayan da lantarki ya katse.

KU KUMA KARANTA: Japan ta jaddada goyon bayanta ga Ukraine akan mamayar da Rasha ta yi mata

Wannan farmakin aka kai da jirage marasa matuƙa da makaman mizal, su ne farmakin da Rasha ta kai mafi girma cikin watanni 3.

Leave a Reply