Ƙasar Iran ta karrama kwamandan da ya kai wa Isra’ila hari
Jagoran Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya karrama kwamandan dakarun kare juyin juya hali da ya jagoranci harin makami mai linzami da ƙasar ta kai wa Isra’ila.
Ayatullah Khamenei ya sanya wa Janar Amirali Hajizadeh aninin Fath (nasara), a ranar Lahadi.
An karrama Janar Amirali Hajizadeh ne saboda “kyakkyawan aiki na ‘Gaskiya’”, in ji shafin rundunar juyin juya halin Musulunci na Iran.
Hajizadeh, mai shekaru 62, ya shugabanci sashin kula da sararin samaniyar rundunar tun lokacin da aka ƙirƙiro shi a shekarar 2009.
KU KUMA KARANTA: Ƙasar Iran ta harba makami mai linzami kan Isra’ila
A ranar Talatar da ta gabata ce rundunar ta harba wasu makamai masu linzami kimanin 200 kan Isra’ila a matsayin ramuwar gayya kan harin da Isra’ila ta kai ta sama da ta kashe shugaban ƙungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah da kuma Janar Abbas Nilforoushan na rundunar a Beirut, babban birnin ƙasar Lebanon.
Wannan dai shi ne hari na biyu kai tsaye da Iran ta kai wa Isra’ila cikin watanni shida.
A watan Afrilu ta kai wani hari da makami mai linzami da jirgin sama mara matuki a matsayin ramuwar gayya kan wani mummunan harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancinta da ke Damascus, babban birnin ƙasar Syria, wanda Tehran ta zargi Isra’ila.
Isra’ila ta sha alwashin mayar da martani bayan harin makami mai linzami da Iran ta kai ranar Talata.