Ƙasar Iran ta harba makami mai linzami kan Isra’ila
A jiya Talata Iran ta harba makami mai linzami kan Isra’ila, abinda ya sabbaba tashin jiniyar ankarar da kawo hari a birnin Tel Aviv da faɗin Isra’ila a cewar ma’aikatar tsaron Isra’ila.
Hakan na zuwa ne ‘yan kwanaki kaɗan bayan Israi’la ta kashe shugaban ƙungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah, da kwamandojinsa.
Hezbollah tace ta harba makamin rokar ne tana harin shelkwatar hukumar leƙen asirin Isra’ila, MOSSAD, wacce take zargi ta kitsa jeren kashe-kashen a kan manyan kwamandojinta a baya-bayan nan da kuma harin fashewar na’urorin sadarwa na makon daya gabata wanda ya hallaka gommai tare da jikkata dubban mutane, ciki harda mambobin ƙungiyar da dama.
Wuta ta haskaka sararin samaniyar Isra’ila kamar yadda ma’aikatan kafar yaɗa labarai ta NBC dake birnin tel aviv da yankin kan iyakar Lebanon na Tyre suka shaida sanda aka harba makami mai linzamin.
KU KUMA KARANTA: Israila ta ƙaddamar da wani hari a tsakiyar Beirut
.An kuma hangi ƙananan tartsatsin wuta, wanda ake zaton sun taso ne daga kariyar kare makamai ta Isra’ila a yayin da kasar ke kokarin kare kanta daga harin.
An kuma jiyo ƙarar wata fashewa a bidiyon da kafar yada labaran ta NBC ta nada, sai dai ba’a tantance ko karar ta haɗuwar makamai masu linzami a sararin samaniya ce ko kuma ta sauƙar makaman ce a cikin isra’ila.
Tunda fari jami’an Amurka sun yi gargaɗin cewar Iran na shirin harin Isra’ila da makami mai linzami, kamar yadda wani babban jami’in fadar White House dana ma’aikatar tsaron Amurka suka shaidawa kafar yada labaran ta NBC a jiya Talata.
Da safiyar yau ne rundunar sojin Isra’ila ta gargaɗi al’ummomin dake zaune a yankunan kan iyakar Lebanon dasu kaurace daga kusan garuruwa 24 bayan da ta kaddamar da samamen da ta ƙira da kwarya-kwaryan kutse ta kasa akan mayakan ƙungiyar Hezbollah.